EFCC Ta Gano Wani Mai Daukar Nauyin Ta'addanci, Kotu Ta Garkame Asusun Bankuna 24

EFCC Ta Gano Wani Mai Daukar Nauyin Ta'addanci, Kotu Ta Garkame Asusun Bankuna 24

  • Hukumar EFCC ta samu izinin rufe asusun bankuna 24 da ake zargi da alaƙar su wajen daukar nauyin ayyukan ta'addanci da safarar kuɗi
  • Kotu ta ba EFCC kwanaki 90 domin kammala bincike kan asusun wani Lawrence Eromosele da ake zargin mai garkuwa da mutane ne
  • EFCC ta ce mutanen da ke da alaƙa da asusun na amfani da dandamalin crypto wajen aikata laifuffuka kamar yadda bincikenta ya nuna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince wa EFCC ta rufe asusun banki 24 da ke da alaƙa da zargin daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Mai shari’a Emeka Nwite ya amince da buƙatar EFCC bayan lauyanta, Martha Babatunde, ta gabatar da roƙon rufe asusun na tsawon kwanaki 90.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe 'yan bindiga 40, aka kama miyagu 916 a jihar Katsina

EFCC ta samu izini daga kotu na garkame asusun bankuna 24 kan zargin ayyukan ta'addanci
Kotu ta ba EFCC kwanaki 90 ta kammala bincike kan asusun bankuna 24 da ta garkame kan ayyukan ta'addanci. Hoto: @officialEFCC
Asali: Facebook

EFCC na binciken masu daukar nauyin ta'addanci

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an gabatar da buƙatar rufe asusun bankin, mai lamba FHC/ABJ/CS/1897/V/2024, ta hannun Ekele Iheanacho, SAN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya nemi izinin rufe asusun bankin da ke karkashin wani Lawrence Lucky Eromosele, wanda ake tuhuma a kan laifin garkuwa da mutane.

EFCC ta bayyana cewa ana binciken asusun bankin kan laifin safarar kuɗi da kuma daukar nauyin ta'addanci ta hanyar dandamalin musayar kuɗin crypto.

Kotu ta rufe asusu 24 kan ayyukan ta'addanci

Lauyan ya bayyana cewa binciken farko ya nuna alaƙar waɗannan asusun da mutanen da ke amfani da dandamalin crypto wajen yi wa Naira zagon ƙasa.

Ya ce akwai buƙatar kare kuɗaɗen da ke cikin asusun yayin da ake ci gaba da bincike da kuma shirin gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu.

Bayan amincewa da rufe asusun, Mai shari’a Nwite ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 24 ga Maris, 2025, bayan lauyan EFCC ya ce za a kammala binciken cikin kwanaki 90.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bankado badakalar CBN, an gano Naira tiriliyan 2.73 da aka karkatar

Ta'addanci: EFCC za ta binciki dan majalisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar EFCC ta ce za ta kama dan majalisar tarayya Aminu Sani-Jaji bisa zargin daukar nauyin ta'addanci a jihar Zamfara.

Ana zargin Hon. Aminu Jaji da daukar nauyin ayyukan ta'addanci a mazabunsa na Kauran Namoda da Birnin Magaji, bisa rahoton da wata kungiya ta shigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.