Ana Korafe Korafe, Gwamnati Ta Fadi Lokacin da Tinubu Zai Nada Mukaman da Ake Jira
- Shugaba Bola Tinubu zai sanar da sunayen jakadun Najeriya da zai nada nan da 'yan makonni, in ji hadiminsa Ademola Oshodi
- Watanni uku da hawansa mulki Tinubu ya dawo da jakadun Najeriya gida, amma bai nada wasu sababbi ba tsawon watanni 16
- Hadimin shugaban kasar ya ce Tinubu yana kan gyara ofisoshin diflomasiyya kafin tura sababbin jakadu zuwa kasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu zai nada sababbin jakadun Najeriya nan da 'yan makonni, in ji wani hadiminsa, Ademola Oshodi.
Ademola Oshodi, babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin waje, ya bayyana hakan a wani shirin talabijin a ranar Lahadi.
Gwamnati ta magantu kan nadin jakadu
A zantawarsa da Channels TV, hadimin shugaban kasar ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina ganin nan da 'yan makonni, za a sanar da sunayen sababbin jakadu, kuma majalisar tarayya za ta fara tantance su domin ba da amincewarsu."
A yayin shirin, tsohon jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Lawrence Obisakin, ya soki rashin nadin jakadu tsawon watanni 16.
A ranar 2 ga Satumba, 2023, watanni uku da hawan mulkin Tinubu, ya dawo da dukkanin jakadun Najeriya daga kasashen da suke aiki.
Ana korafi kan rashin nada jakadu
A lokacin, ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ya ce nadin jakadu ko dawo da su gida wani hakki ne na shugaban kasa.
Sai dai, har yanzu shugaban bai gabatar da jerin sunayen sababin jakadu ga majalisa don tantancewa ba, lamarin da ya jawo korafe-korafe.
A wannan karon, Oshodi ya ce shugaban yana kokarin shiryawa kafin tura jakadun zuwa kasashen waje.
"Ana gyara ofisoshin diflomasiyya" - Oshodi
Mai taimakawa shugaban kasar ya kara da cewa:
"Nan da 'yan makonni za a ga sunayen jakadun, amma tuni aka aika wasu manyan wakilai don fara aiki kafin zuwan jakadun."
Ya ci gaba da da cewa:
"Ofisoshin diflomasiyya suna cikin wani yanayi na bukatar gyara kuma gwamnati na aiki a kan hakan saboda ta gaji matsaloli da dama a ofisoshin."
Oshodi ya ce, ko a gwamnatin baya, an dauki watanni 20 kafin a nada jakadu.
Illolin rashin nada jakadun Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai naɗa sababbin jakadu ba tun bayan dawo da tsofaffin gida a 2023, abin da masana ke gargadi a kai.
Masana diflomasiyya dai sun bayyana damuwa kan rashin nadin jakadun, suna cewa hakan na kawo cikas ga dangantakar Najeriya da sauran kasashe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng