Tinubu Ya Amince a Kafa Sabuwar Jami'a a Kudancin Kaduna, Shettima Ya Yi Bayani

Tinubu Ya Amince a Kafa Sabuwar Jami'a a Kudancin Kaduna, Shettima Ya Yi Bayani

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna domin magance bukatun ilimi da ci gaban yankin
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana haka tare da cewa ana duba kafa cibiyar lafiya a Kafanchan, jihar Kaduna
  • Shettima ya jaddada goyon bayan Tinubu ga ci gaban Kudancin Kaduna, yana kuma yabawa gwamnatin jihar karkashin Uba Sani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa jami'ar tarayya a Kudancin Kaduna domin samar da ci gaba tare da magance bukatun ilimi a yankin.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya bayyana hakan ya ce ana duba yiwuwar kafa cibiyar lafiya ta tarayya a Kafanchan, jihar Kaduna.

Kashim Shettima ya yi magana kan shirin Tinubu na gina sabuwar jami'a a Kudancin Kaduna
Kashim Shettima ya yiwa 'yan Kudancin Kaduna albishir da amincewar Tinubu na kafa jami'a a yankin. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya amince a kafa jami'a a Kaduna

Kara karanta wannan

"Carter mai son cigabanmu ne," Tinubu ya yi jimamin mutuwar tsohon shugaban Amurka

The Nation ta rahoto Shettima ya fadi hakan ne a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Kukah bisa rasuwar mai martaba Yohanna Sidi Kukah, Agwom Akulu na masarautar Ikulu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa daga Stanley Nkwocha, ta ce Shettima ya tuntuɓi Shugaba Bola Tinubu, wanda ya amince da kafa jami'ar.

Shettima ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen ganin an kawo ci gaba a Kudancin Kaduna, musamman a fannin tsaro.

Ya bayyana cewa nada Janar Christopher Musa a matsayin shugaban ma'aikatan tsaro na kasa ya nuna kulawar shugaban kasa ga yankin.

Kashim Shettima ya yabawa gwamnan Kaduna

Mataimakin Shugaban kasa ya tabbatar da cewa Tinubu na da niyyar ganin mutanen Kaduna suna samun ci gaba.

Kashim Shettima ya kuma yaba wa Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, kan yadda yake gudanar da mulki tare da hada kan jama'a.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta yi aiki tare da gwamnatin Kaduna wajen ganin cewa al'ummar jihar sun samu ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu a Legas, an ji abin da suka tattauna a cikin bidiyo

Shettima ya yi alkawarin inganta hanyoyin sufuri a yankin Kudancin Kaduna da kuma samar da karin ayyuka ga matasan yankin.

Za a kirkiri jami'ar Tinubu ta musamman

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar tarayya tana kokarin kafa sabuwar jami'a da sunan Bola Tinubu, domin bunkasa ilimi da kuma inganta harshen gida a Najeriya.

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu, ya jagoranci gabatar da kudirin tare da wasu 'yan majalisa takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.