Taraba: Yadda Wasu Malaman Musulunci Suka Shiga Coci domin Bikin Kirsimeti
- Tawagar malaman Musulunci ta ziyarci wata coci a Taraba domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa
- Malaman sun bayyana cewa sun kai ziyarar ne da nufin inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin bangarorin addinan biyu
- Shugaban cocin, Fasto Samuel Omajali wanda ya nuna jin dadi da ziyarar malaman ya ba da tabbacin hadin kansu ga zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Wata tawagar malaman Musulunci karkashin jagorancin Alhaji Hussaini Ismail ta ziyarci Fasto Samuel Omajali na cocin Deeper Life, jihar Taraba.
Alhaji Hussaini Ismail shi ne mai ba gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas shawara kan harkokin addinin Musulunci.
Taraba: Malaman Musulunci sun ziyarci coci
Mai ba gwamnan shawarar ya ce sun kai wannan ziyarar ne a ranar Lahadi domin domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Kirsimet, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Hussaini ya bayyana cewa tawagar ta kuma kai ziyarar domin domin inganta zaman lafiya da fahimta tsakanin bangarorin addinan biyu a lokacin bikin Kirsimeti.
“Wannan ziyarar ta nuna muhimmancin tattaunawar addini wajen gina fahimtar juna da tabbatar da zaman lafiya.”
- Inji Alhaji Hussaini.
Fasto ya yabawa malamai da zuwa coci
A nasa bangaren, Fasto Omajali ya jaddada bukatar hadin kai domin ganin an cimma burin Gwamna Kefas na jihar Taraba ta zamo tsintsiya madaurinki daya.
Ya kara da cewa,
“Idan muka hada kai, za mu iya gina al’umma da ta dogara da girmama juna da mutunta dabi’unmu na bai daya.”
Fasto Omajali ya yi imanin cewa wannan ziyara mataki ne mai kyau wajen tabbatar da shugabanci nagari da karfafa hadin kai tsakanin addinan biyu.
'Yan Shi'a sun halarci bikin cocin Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa mabiya akidar Shi'a a jihar Kaduna sun halarci bikin Kirsimeti a cocin St. Joseph da ke yankin Samarun Zariya.
Yan kungiyar Shi’ar karkashin jagorancin Farfesa Isah Hassan Mshelgaru sun bayyana cewa sun ziyarci cocin domin nuna abota da zaman lafiya da Kiristocin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng