Abun mamaki: Musulmai sun je coci domin taya Kiristoci bikin Kirsimeti (hoto)

Abun mamaki: Musulmai sun je coci domin taya Kiristoci bikin Kirsimeti (hoto)

- Musulmai sun yi bikin Kirsimeti tare da Kiristoci a jihar Nasarawa

- Hakan ya ba mutane da dama da basu taba kawo kan cewa hakan zai faru ba mamaki

- Yan Najeriya sun yi martani daban daban kan cci gaban

A wani yunkuri da ba kasafai yake faruwa ba a wannan duniya, wasu Musulmai sun yi watsi da al’ada sannan suka shiga sahun Kiristoci domin yin bikin haihuwar Yesu Almasihu.

Yan uwa Musulmai na Shia reshen jihar Nasarawa sune suka yi wannan yunkuri, Tribune ta ruwaito.

Sun ziyarci cocin Evangelical Reformed Church of Christ (ERCC), Graceland Lafia, jihar Nasarawa domin nuna goyon bayansu ga al’umman Kirisa, Tribune ta ruwaito.

Abun mamaki: Musulmai sun je coci domin taya Kiristoci bikin Kirsimeti (hoto)
Abun mamaki: Musulmai sun je coci domin taya Kiristoci bikin Kirsimeti Hoto: Nigerian Tribunel
Asali: UGC

A cewar Mallam Muhammad Amin, Shugaban kungiyar, sun je coci ne domin yiwa kasar da jihar Nasarawa addu’an samun sauki tare da taya Kiristoci murnar haihuwar Yesu Almasihu.

KU KARANTA KUMA: Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani

A cewarsa, haihuwar Yesu Almasihu na da muhimmanci ga jama’a saboda haka akwai bukatar tayasu murna cikin kauna kamar yadda yake a tsarkakan littafi inda ya kara da cewar addinan guda biyu sun yarda cewa Yesu Almasihu ma’aikin Allah ne.

Hakan ya janyo martani da dama a soshiyal midiya inda mutane da dama suka jinjinawa kungiyar Musuluncin.

Emmanuel Akpan ya rubuta a Facebook:

“Ma shaa Allah. Wannan abu yayi kyau. Allah ya ci gaba da yi musu albarka. Dukkanmu mun yarda da Allah daya.”

Benjamin Ronald Chukwuma a bangarensa ya ce:

“Daya daga cikin manyan matsalolin Najeriya a yau shine rashin juriya na addini...Kuma yana taka rawar gani a rayuwar kasarmu.”

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu

Matthew Ighodalo ya kara da cewa:

"Allah yayi musu albarka Kirista da Musulmai duk daya ne.”

A wani labarin, Jaridar Sahelian Times ta fitar da rahoto cewa malamin jami’ar ABU Zaria da aka sace, Dr. Ibrahim G. Bako, ya samu ‘yanci har ya koma gida.

Ibrahim G. Bako wanda aka dauke har gida a ranar 23 ga watan Nuwamba ya shafe wata guda cur a hannun masu garkuwa da mutane kafin ya fito.

Idan za ku iya tunawa an bi wannan Bawan Allah ne har gidansa da ke unguwar BZ a cikin jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Samaru, aka yi gaba da shi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel