Musulmai Sun Taya Kiristoci Bikin Kirsimeti a Jihar Bauchi

Musulmai Sun Taya Kiristoci Bikin Kirsimeti a Jihar Bauchi

  • Domin karfafa zumunci da zaman lafiya, al'ummar Musulmai sun taya yan uwa Kiristoci bikin Kirsimeti a jihar Bauchi
  • Yan uwa Musulman sun ziyarci cocin Yalwan Kagadama inda suka rera wakoki tare da gabatar da kyaututtukan Kirsimeti ga cocin
  • Sun yi tuni a kan muhimmacin hadin kai tsakanin addinan guda biyu domin ci gaban kasar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Wasu al'ummar Musulmai a jihar Bauchi sun ziyarci cocin Yalwan Kagadama da ke Bauchi a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, don raya Kiristoci murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu.

Musulman wadanda sun yarda cewa hadin kai tsakanin addinan guda biyu da da muhimmanci don ci gaban kasar don haka suka yi kira ga kulla dangantaka mai kyau.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun yi bikin Kirsimeti ba tare da albashin Disamba ba

Musulmai sun ziyarci coci
Musulmai Sun Taya Kiristoci Bikin Kirsimeti a Jihar Bauchi Hoto: ait.live
Asali: UGC

Ait.live ta rahoto cewa ziyarar da ka kai cocina a garin Bauchi ya nuna cewa an yi bikin Kirsimeti cikin lumana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cocin Kagadama Bauchi, wasu Musulmai sun hallara domin taya Kiristoci murna, inda suka aika sakon hadin kai yayin da suka rera wakoki da gabatarwa cocin kyaututtukan Kirsimeti.

Wasu malaman addini, sun ce akwai bukatar shugabannin Najeriya su cusa dabi'ar Tawali'u domin ceto yan Najeriya daga halin da suke ciki, kamar yadda Annabi Isah ya zo don ceto al'umma.

Ba tare da la'akari da kalubalen da ake ciki ba, Kiristocin da ke cikin farin ciki sun yin yan raye-raye tare da gabatar da kyaututtukan Kirsimeti.

Masu bautan sun yarda cewa duk da tarin kalubalen da kasar ke ciki, cocin zai ci gaba da yabon Allah a wakokin yabo, inda suka yarda cewa Allah zai ceto Najeriya wata rana ya kuma samar da mafita daga matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Kirsimeti: Yan Shi'a sun halarci bikin a coci, sun fadi kwararan dalilai masu kama hankali

Gwamnan Bauchi ya daukarwa Kiristoci alkawari

A gefe guda, Gwamnan jihar Bauchi Sen Bala Mohammed ya tabbatar wa mabiya addinin kirista a jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin kawo sauyi a fadin jihar, rahoton Nigerian Tribune.

Gwamnan ya jaddada cewa hakan ya biyo bayan gagarumin goyon bayan da kungiyar kiristoci ke bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai a fadin jihar.

Ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar Kiristoci a gidan gwamnati a ziyarar ban girma da suka kai masa na ranar Kirsimeti.

Sanwo-Olu ya shiga masallacin Juma'a

A wani labarin, mun kawo cewa a ranar Alhamis ce 21 ga watan Disamba Shugaba Bola Tinubu ya dira a Legas don gudanar da bikin Kirsimeti.

Zuwan shugaban ya samu tarba mai kyau daga yaron dakinsa kuma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Legit ta tattaro.

Sanwo-Olu ya kuma kasance tare da shugaban a duk inda zai je musamman wasu ayyuka ko wurin taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel