Yadda Gwamnatin Najeriya ta Kashe N1.4bn Kan Tubabbun ’Yan Ta’adda

Yadda Gwamnatin Najeriya ta Kashe N1.4bn Kan Tubabbun ’Yan Ta’adda

  • Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da kashe makudan kudade don tabbatar tsoffin ‘yan ta’adda sun dawo kan turba
  • Rahoto ya tono yadda cikin watanni 18 aka kashe makudan kudade domin gine-gine da gyaran hali ga ‘yan ta’addan
  • An kawo doka tare da kafa cibiyar yaki da ta’addanci tun a zamanin Buhari, kuma ana ci gaba da sukar aikin na gwamnati

Najeriya - Gwamnatin Tarayya ta kashe kusan naira biliyan 1.4 wajen daow da tubabbun ’yan ta’adda kan turba da kafa cibiyoyin gyaran a Najeriya cikin watanni 18 da suka gabata.

Wannan kudin ya shafi gyaran wuraren gwaji da kuma gine-ginen da ake amfani da su don sake fasali da halin tsoffin ‘yan ta’addan Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci.

Idan baku manta, a lokuta da dama, gwamnatin Najeriya ta sha karbar tsoffin ‘yan ta’adda tare da bayyana yi masu afuwa duk da aikata laifukan da suka yi a baya.

Kara karanta wannan

Talakawa sun yi tururuwa gidan Tinubu neman tallafi, an caccaki shugaban kasa

Yadda gwamnatin Najeriya ta kashe kudi kan 'yan ta'adda
Farfado da halin 'yan ta'adda ya cinyewa Najeriya kudi | Hoto: FB/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Dalilin kashe wadannan kudaden

A tun farko, gwamnatin Buhari ta kafa Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC) domin tabbatar da tsaro a kasar baki daya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan ne aka fara shirye-shiryen gyaran hali ga tsoffin ’yan ta’adda tare da kafa sabbin cibiyoyin gyaran hali a kasar.

An samu lokuta da dama da gwamnatin ke bayyana tasirin wadannan cibiyoyi da tace sun taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci.

Yadda aka kashe kudaden cikin watanni 18

Sai dai, bayanai daga GovSpend, wata kafar bin diddigin kashe-kashen kudin gwamnati, sun nuna cewa tsakanin Disamba 2022 da Mayu 2024, Ma’aikatar Shari’a ta kashe Naira biliyan 1.4 wajen gina cibiyoyin gyaran hali ga tsoffin ’yan ta’adda da gyaran gine-gine don gudanar da shari’o’in ta’addanci.

Wannan kashe kudin ya kunshi:

  1. 27 ga Maris, 2023: An saki Naira miliyan 612 ga wasu kamfanoni uku don gyaran gine-gine domin gudanar da shari’o’in, tare da gina dakunan kwana ga tsoffin ’yan ta’adda a karkashin shirin Operation Safe Corridor.
  2. 2024: An tura Naira miliyan 179 ga wasu kamfanoni uku domin ayyuka kamar samar da kwamfutoci da kayan aikin da ake amfani da su wajen gabatar da shari’o’in ta’addanci.

Kara karanta wannan

Jihohin Najeriya sun yi kasafin sama da N74trn don magance talauci a 2025

Tattaunawar da ake kan shirin

Sai dai, wasu masana tsaro sun nuna damuwa kan yadda ake gudanar da wannan shirin na maido da tsagerun ‘yan ta’adda kan turba.

Wasu suna ganin cewa kashe wannan makudan kudade kan tsoffin ‘yan ta’adda ba zai kawo gyara sosai ba, yayin da wasu ke kare shirin a matsayin hanya mai kyau don rage ayyukan ta’addanci a kasar.

Har yanzu dai ana ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan wannan lamari, ga kuma har yanzu ana samun bullar sabbin ‘yan ta’adda a kasar.

amman ganin yadda jama’a ke nuna damuwa kan amfani da makudan kudaden gwamnati wajen gyara tsoffin masu laifi, maimakon mayar da hankali kan ’yan kasa masu bukatar tallafi.

Ana zargin wasu 'yan siyasa da daukar nauyin ta'addanci

A wani labarin, an zargi wasu 'yan siyasa da shugabanni a Najeriya da hannu a ayyukan ta'addancin da ke faruwa yanzu.

Kara karanta wannan

Babban malami a Arewa ya dura kan gwamnati, ya ce ita ta jawo rasa rayuka a jihohi 3

Wani rahoton da aka wallafa ya bayyana cewa, akwai hannayensu ta hanyoyi da dama, shi yasa lamarin ke ta'azzara.

Sai dai, wannan zargi ne kawai da ba za a iya tabbatar dashi ba duba da wasu maganganun da suke kan aikin yaki da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.