NAFDAC Ta Kwace Jabun Kayayyaki na Naira Biliyan 140, Ta Fadi Yadda Ta Yi da Su

NAFDAC Ta Kwace Jabun Kayayyaki na Naira Biliyan 140, Ta Fadi Yadda Ta Yi da Su

  • NAFDAC ta lalata kayayyakin da aka kama na Naira biliyan 120 tsakanin watan Yuli zuwa Disamba domin kare lafiyar 'yan kasa
  • Hukumar ta ja hankalin jama’a kan siyan magunguna da abinci marasa shaidar rajista domin kauce wa hatsari da illoli ga lafiya
  • A Nasarawa, NAFDAC ta kama shinkafa ta jabu, ta rufe shaguna 150 a Aba saboda kama jabun kayayyaki da darajarsu ta kai N5bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar NAFDAC ta sanar da lalata kayayyaki da aka kama na sama da Naira biliyan 120 a tsakanin watan Yuli zuwa Disambar 2024.

An lalata kayayyakin ne a shiyyoyi shida na ƙasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja domin kare lafiyar 'yan Najeriya daga mtsalar lafiya.

Hukumar NAFDAC ta yi magana kan kayayyakin jabu da ta kama a shekarar 2024
NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu da ta kama na Naira miliyan 140 a cikin 2024. Hoto: @NafdacAgency
Asali: Twitter

NAFDAC ta aika sakon Kirsimeti

Hukumar ta tabbatar wa da 'yan kasa cewa tana daukar matakan kare lafiyarsu kafin, yayin, da bayan bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato suka jawo muka jefa masu bam Inji Sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana hakan a cikin sakon bikin Kirsimeti, wanda Sayo Akintola ya sanyawa hannu.

Farfesa Adeyeye ta ja hankalin 'yan Najeriya da su dinga siyan abinci da abin sha daga wuraren da za a iya gano adireshinsu don sauƙaƙe sa-ido.

NAFDAC tana bincike kayayyaki marasa kyau

Ta gargadi mutane kan siyan magunguna da abinci marasa lamba ta rajista daga hukumar NAFDAC, tana cewa mafi sauƙin kaya sun fi hatsari.

Hukumar ta ci gaba da bincike kan magunguna marasa inganci da kayan abinci marasa kyau, tana share kasuwanni don tsabtace kayayyakin da aka yi masu jabu.

Ma'aikatan hukumar suna aiki tukuru a fagen kama magunguna, giya da abinci marasa inganci da ke iya yin illa ga lafiyar jama’a.

NAFDAC ta lalata kayayyakin biliyoyin Naira

A watan Disamba kadai, hukumar ta lalata magunguna marasa inganci da kudinsu ya kai Naira biliyan 11 a Ibadan, da wasu jabun kayayyaki a Legas.

Kara karanta wannan

"Akwai kullin arziki a 2025," Ganduje ya nemi a kara yi wa Tinubu uziri

A jihar Nasarawa, NAFDAC ta gano wata masana’anta da ke cike shinkafa ta jabu, inda ta kama buhu sama da 1,600 na Naira biliyan 5.

Haka kuma, ta rufe shaguna 150 a Aba, jihar Abia, a yunkurin dakile ayyukan sarrafa kayayyakin jabu da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.

NAFDAC ta tattaro jabun magunguna a Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu, marasa inganci da waɗanda suka lalace da darajarsu ta kai N985.3m a Kano.

Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce kawar da magungunan marasa inganci zai taimaka wajen inganta lafiyar 'yan Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.