Yan Nigeria na cin shinkafar dabbobi da ta lalace -Lai Mohammed
- Ana shigo da shinkafar da ta lalace Nigeria ta barauniyar hanya
- Dabbobi ne ya kamata su rinka amfani da ita, kasancewar ta yi sama da shekaru shida a ajiye
- Yan Nigeria zasu wadata da shinkafa yar gida nan da shekara daya da rabi
Ministan Labarai Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana damuwarsa akan yadda ake shigowa da shinkafar data lalace Nigeria daga wasu kasashe, inda yace dabbobi ne ya kamata su yi amfani da ita ba mutane ba.
Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa dake Oro, Ministan ya dora laifin hakan ga safarar kaya da akeyi ta barauniyar hanya, yana mai nuni da cewa inda an shigo da shinkafar ta hanyar data dace, to da tuni hukumar NAFDAC ta dakatar da ita.
"Shinkafar da ake shigowa da ita yanzu ta dauki sama da shekaru shida a ajiye, wanda yasa ta lalace. Zata zamo illa ga mutane idan akayi amfani da ita." A cewar sa.
KU KARANTA WANNAN: Layyar manya: Wani balarabe yayi layya da dan akuyan Riyal miliyan 13
Ministan labaran ya ce ana sayar da shinkafar cikin farashi mai rahusa, saboda an san cewa rubabbiya ce; dabbobine kawai ya kamata suyi amfani da ita.
Ya ce: "Ana fasa kwabrin shinkafa ne ta barauniyar hanya saboda gaza cika sharudan hukumar NAFDAC. Babu wata shinkafa yar gida da takai sama da shekara a ajiye, amma shinkafar da ake shigowa da ita ta zarce sama da shekaru shida a kasar da aka dauko ta"
Sai dai Lai Muhammad yayi alkawarin cewa nan da shekara daya da rabi, 'yan Nigeria zasu zamo masu wadatuwa da shinkafa, ganin irin kokarin gwamnati na bunkasa nomanta a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng