Abin Alheri da Gwamnan Kano Ya Yi wa Matashin da Ya Lashe Gasar Alƙur'ani Ta 2024

Abin Alheri da Gwamnan Kano Ya Yi wa Matashin da Ya Lashe Gasar Alƙur'ani Ta 2024

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya taya Buhari Sunusi Idris murna bisa lashe gasar karatun Alkur'ani ta ƙasa
  • Buhari Sanusi wanda ya wakilci jihar Kano a gasar da ta samu wakilai daga jihohi 34 ya lashe gasar ne da kashi 98.2 cikin 100
  • Gwamnan Kano wanda ya ba Buhari kyautar kujerar Hajji ya kuma bayyana shirin da ya yi domin girmama nasarar matashin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya Buhari Sunusi Idris murnar zama zakaran maza a gasar karatun Alkur'ani ta ƙasa a 2024.

A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, Buhari, wanda ya wakilci Kano, ya lashe gasar da kashi 98.2%.

Abba ya yi magana kan matashin Kano da ya lashe gasar Al-kur'ani ta 2024
Abba zai shirya walima ga matashin da ya lashe gasar karatun Alkur'ani ta 2024. Hoto: Faruk Goni Kabir Ya'kub, Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Sanarwar da Sanusi Bature ya fitar a shafinsa na Facebook ta nuna cewa an gudanar da wannan gasar ta 2024 a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu a Legas, an ji abin da suka tattauna a cikin bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya ba matashi kyautar kujerar Hajji

Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa kan nasarar Buhari wanda ya samu kyautar kujerar aikin Hajji tun a lokacin da aka sanar da cewa shi ya lashe gasar Alkur'anin.

Haka zalika, sanarwar ta ce gwamnan na Kano na shirye-shiryen gudanar da walima ta musamman don taya Buhari murna.

Gwamnan ya bayyana cewa Kano na ci gaba da zama "gidan karatun Alkur'ani," tare da jaddada matsayin jihar a fagen karatun addinin Musulunci.

Abba ya yi murnar nasarar matashin Kano

Yayinda ake murnar nasarar Buhari, gwamnan ya karfafawa matashin gwiwa da ya ci gaba da yada koyarwar Alkur'ani.

Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su kara yin addu'a domin samun zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a Najeriya.

Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin Alkur'ani a rayuwar Musulmi, yana kira da su rike shi a matsayin tushen shiriya, jin dadi da zama haske a cikin duhu.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi shirinsu bayan iftila'in harin bam a Sokoto, ya ba da gudunmawar kudi

Ganduje ya karrama gwarzon gasar Alkur'ani

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi goma sha tara ta arziki ga wadanda suka lashe gasar Alkur'ani a jihar.

Ganduje, wanda shi ne shugaban APC na kasa, ya ba da kyautar kujerun Hajji ga wadanda suka shiga sahun farko a gasar sannan ya raba masu motoci da Keke Napepe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.