Lalacewar Wuta, Rikicin Masarautar Kano da Wasu Abubuwa 10 da Suka Mamaye 2024
FCT - Shekarar 2024 ta zo da manyan abubuwan da suka shafi fannoni daban-daban ; daga siyasa, tabarbarewar tattalin arziki zuwa rikicin sarauta da sauransu.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yayin da duniya ke kusantar 2025, Legit.ng Hausa ta duba muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin shekarar 2024.
Ga jerin manyan abubuwa 10 da suka mamaye shekarar 2024:
1. Fashewar bama bamai a Ibadan
Shekarar 2024 ta fara da rashin jin daɗi yayin da aka samu fashewar bam a Ibadan a daren ranar Talata, 16 ga Janairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da dama suka jikkata a sakamakon fashewar bam din a wani gida a jihar Oyo.
Gidaje da dama sun samu matsala sakamakon fashewar, yayin jami'an tsaro suka gudanar da aikin ceton mutanen da abin ya shafa.
2. Canjin taken ƙasa
A watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar da ta mayar da tsohon taken ƙasa wanda aka fara amfani da shi a 1978.
Taken, wanda Lillian Jean Williams ta rubuta shi a 1959 kuma Frances Berda ya tsara waƙar ya fara ne da kalmomin "Nigeria, We Hail Thee."
3. Rikicin masarautar Kano
Rikicin masarautar Kano ya faru a 2024 tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Rikicin ya fara ne a Mayu lokacin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya maido Sanusi a matsayin sarki.
Sanusi II ya koma kan mulki bayan soke dokar masarautar Kano da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige shi a 2020.
4. Durkushewar tashar wutar lantarki
Legit Hausa ta rahoto cewa tashar wutar lantarkin Najeriya ta durkushe akalla sau 12 a 2024, wanda ya haifar da yawan daukewar wuta a sassan ƙasar.
Wannan matsalar ta haifar da damuwa game da ingancin tsarin samar da makamashi na ƙasa duk da kokarin da TCN ke yi na magance matsalar.
5. Tsare Simon Ekpa
A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, jami’an binciken Finland sun kama Simon Ekpa bisa zargin ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Ana zargin Simon Ekpa da tada zaune tsaye da kuma niyyar aikata laifuffuka masu alaka da ta’addanci.
6. Takaddamar gyaran haraji
Takaddama ta barke a Najeriya bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar da kudurorin gyaran haraji.
Wasu sun zargi tsarin da rashin adalci, inda gwamnonin arewa suka bukaci a janye kudurorin yayin da gwamnati ta dage kan amfanin gyaran.
7. Ambaliyar ruwa a Borno
An samu mummunar ambaliyar ruwa a Borno bayan fashewar Dam din Alau a ranar 10 ga Satumba, 2024.
Fiye da mutane miliyan ɗaya ne ambaliyar ruwan ta shafa yayin da gidajen Maiduguri suka nutse a cikin ruwan kuma aka samu asarar rayuka.
8. Zanga-zangar adawa da gwamnati
An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati tsakanin 1 zuwa 10 ga Agusta, 2024, sakamakon ƙararuwar tsadar rayuwa a Najeriya.
Duk da gwamnati ta nuna rashin amincewa, masu zanga-zanga sun rufe kasar a cikin wadannan kwanaki, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dukiya.
9. Tsare kananan yaran Arewa
A watan Nuwamba ne aka gurfanar da kananan yaran Arewa masu yawa a kotu, inda aka samu yara 'yan shekara 14 zuwa 18 a cikin wadanda ake zargin.
Gwamnati ta zargi yaran da take dokokin kasa lokacin zanga zanga, lamarin da ya jawo mata suka tare da samun matsin lamba har sai da Tinubu ya sa kotu ta sallame su.
10. Turmutsutsu a wajen karbar tallafi
Mummunar turmutsutsu ya faru a Ibadan, Anambra da Abuja yayin rabon abinci a watan Disamba, 2024, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Gwamnatin tarayya ta dauki zafi sosai yadda aka samu asarar rayuka a ire-iren wadannan tarukan rabon tallafin, inda har ta gindayawa masu son yin rabo sharudda.
'Yan siyasa 6 da suka koma APC a 2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gawurtattun 'yan siyasar Najeriya shida da aka sansu a bangaren adawa sun ajiye adawarsu tare da komawa jam'iyyar APC.
Mukhtar Ramalan Yero na daga cikin manyan 'yan siyasar kasarnan shida da suka fice daga jam'iyyarsu tare da magoya bayansu zuwa APC a cikin shekarar 2024.
Asali: Legit.ng