Zo Ka Nema: Hukumar Kwastam Ta Fara Daukar Sababbin Ma'aikata, Ta Gindaya Sharudda
- Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta fara daukar sababbin ma'aikata domin cike guraben aiki a matakai daban-daban
- Za a fara cike neman aiki daga ranar 27 ga Disamba, 2024 zuwa ranar 2 ga Janairu, 2025, tashafin daukar ma’aikata na NCS
- 'Yan Najeriya da Legit Hausa ta tattauna da su sun roki hukumar da ta kara wa'adin cike aikin domin ba mutane masu yawa dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja — Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta fara daukar sababbin ma'aikata domin cike guraben aiki a mukamai daban-daban.
A cewar bayanan da ke kan shafinta na yanar gizo, NCS tana daukar ma’aikata a kan mukamai uku masu muhimmanci.
Mukaman da hukumar NCS ta sanar a shafinta na yanar gizo tana dauka su ne kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Rukunin Superintendent
- Rukunin Inspectorate
- Rukunin Customs Assistant
Aikin Kwastam: NCS ta gindaya sharuɗɗa
Rahotanni sun nuna cewa dole ne masu neman aiki a rukunin Superintendent su mallaki digiri na Jami’a ko HND (Higher National Diploma) tare da takardar sallama ta NYSC.
Dole ne masu neman aiki a rukunin Inspectorate su kasance suna da Diploma na Kasa (ND) ko NCE daga makarantar da aka amince da ita.
A cewar hukumar NCS, masu neman aiki a rukunin Customs Assistant suna buƙatar takardar O'Level (WAEC ko NECO) kawai.
Baya ga shaidar karatu, NCS ta ce dole ne duk masu neman aikin dole ne su kasance cikin koshin lafiyar jiki da kwakwalwa tare da gabatar da shaida daga asibiti na gwamnati.
Aikin Kwastam: NCS ta bude shafin yanar gizo
Tsarin neman aikin zai fara ne daga ranar Juma’a, 27 ga Disamba, 2024, kuma zai kare a ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025.
Masu sha'awar neman aikin za su iya yin rijista ta hanyar shafin yanar gizon hukumar a: https://recruitment.customs.gov.ng
Aikin Kwastam: NCS ta gargadi masu neman aiki
A halin da ake ciki, NCS ta yi kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan da masu damfara da za su iya cutar masu masu neman aikin ba tare da an gane ba.
"Ku yi hattara da masu damfara! Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) tana tunatar da ‘yan Najeriya cewa tsarin daukar ma’aikatanta kyauta ne."
"Ba mu karbar ko sisi a kowane mataki na tsarin daukar ma’aikata. Idan wani ya bukaci ku biya kudi, to dan damfara ne. Kada ku fada tarkon masu damfara!"
- A cewar hukumar NCS.
"Allah ya sa gwamnati ta kiyaye" - Abdullahi
A zantawarmu da Abdullahi Kabir Maiwada, wani matashi a Katsina ya ce yana fatan gwamnatin tarayyar za ta dauki matakan da zai sa 'ya'yan talaka su samu aikin.
"Mun sha ganin yadda hukumomin gwamnati ke fitar da sanarwar daukar aiki, amma a karshe 'ya'yan masu hannu da shuni da masu kafa ne ake ba aikin.
"Wasu lokutan sai ka je ka samu horo, ka cike dukkanin ka'idojin da ake bukata, amma ranar da aka kafe sunayen wadanda aka ba aikin, sai ka ga ba sunanka."
- A cewar Abdullahi.
Shi kuwa Salim Ashiru magana ya yi a kan wa'adin da aka diba na cike aikin, inda ya roki hukumar NCS da ta kara wa'adin da mako guda.
Abdullahi ya ce:
"An fara cike neman aikin ne a lokacin da mutane ke hutun karshen shekara, da yawa sun tafi kauyuka hutu wanda ba zai ba su damar cikewa ba.
"Muna rokon hukumar ta kara wa'adin cike aikin ko da da mako daya ne gaskiya, don ba mutane damar yin rijista."
Hukumar FIRS za ta dauki ma’aikata
A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar tara kudin shiga ta tarayya (FIRS) ta sanar da cewa za ta fara daukar sababbin ma'aikata a matakan aiki daban daban.
Hukumar FIRS ta bayyana cewa tane neman matasan da suka kammala karatun gaba da sakandare domin su nemi aikin jami'an haraji a hukumarta.
Asali: Legit.ng