A lura a gane: Jerin sharudda 10 da hukumar kwastam ta gindaya ma masu son shiga aikin kwastam

A lura a gane: Jerin sharudda 10 da hukumar kwastam ta gindaya ma masu son shiga aikin kwastam

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, wanda ake kira da Nigeri Customs a turance ta sanar da gayyatar masu sha’awar neman aikin dasu fara cike ciken nuna muradinsu na shiga aikin a shafinta na yanar gizo, kamar dai yadda aka saba.

Babban mataimakin kwanturola mai kula da sha’anin ma’aikatan hukumar, Umar Sunusi ya tabbatar da haka a ranar Laraba, inda yace daukan aikin ya samu amincewar majalizar zartarwar Najeriya, inda yace hukumar zata dauki sabbin ma’aikata dubu uku da dari biyu (3,200).

KU KARANTA: Yadda wani Magidanci ya saki matansa 2 a lokaci guda saboda fitina

Sai dai hukumar ta gindaya wasu sharudda na musamman guda goma da take bukatar duk masu sha’awar shiga aikinta su sani, kuma su cikasu, domin ta haka ne kawai hukumar zata duba yiwuwar daukansu aikin;

- Ka kasance haifaffen dan Najeriya ko ta asali

- Kada Namiji yayi kasa da tsawon mita 1.7, mace kuma 1.64

- Fadin kirjin Namiji kada ya gaza mita 0.87

- Samun takardar shaidar cikakken lafiya daga Asibitin gwamnati

- Ya kasance baka da wata nakasa ko tabin hankali

- Ya kasance babu mai binka bashin kudi ko makamancin matsalar kudi da jama’a

- Ya kasance ba’a taba kamaka da aikata miyagun laifuka ba

- Gabatar da shaidar zama dan kasa dauke da sa hannun shugaban karamar hukuma ko sakatare

- Dama daya za’a bayar na neman aikin, don haka a kiyaye

- Shiga shafin yanar gizo na https://www.vacancy.customs.gov.ng don neman aikin

Mu daga nan Legit.ng sai dai muce Allah Ya baiwa mai rabo sa’a, kuma Ya shigar da masu kishin kasa cikin wannan aikin domin kawo ingantaccen gyara da garambawul a aikin hukumar, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng