Najeriya da China Sun Sabunta Yarjejeniyar $2bn da Ake Fatan Za Ta Karya Tasirin Dala
- Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta sake yin akalla shekaru uku ta na musayar Naira da Yuan da kasar Sin
- Babban bankin Sin (PBOC) ya sanar da cewa an sabunta yarjejeniyar da aka fara saw a hannu a Yulin 2018
- Manufar wannan tsari ita ce Najeriya ta rage wahalar da ta ke sha wajen mu’amala da kudi irinsu Dalar Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja – Gwamnatin Najeriya da Kasar Sin sabunta yarjejeniyar kudi wanda darajarta ta kai Yuan biliyan watau dala biliyan 2.
An yi wannan ne da nufin bunkasa kasuwanci da alakar da ke tsakanin Najeriya da ke Afrika ta yamma da kasar da ke Asiya.

Source: Getty Images
An sabunta yarjejeniyar Najeriya da China
Bloomberg ta ce babban bankin kasar Sin watau PBOC ya tabbatar da yarjejeniyar za ta cigaba da aiki na tsawon shekaru har uku.

Kara karanta wannan
Matawalle ya fadi shirinsu bayan iftila'in harin bam a Sokoto, ya ba da gudunmawar kudi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin da PBOC ya fitar ya ce akwai damar sabunta yarjejeniyar idan wa’adi ya cika.
Yarjejeniyar ta ba da damar a rika ciniki tsakanin kasashen biyu da kudin Naira da Yuan, wannan zai sa a huta da wahalar Dala.
Yadda Najeriya ta shiga yarjejeniya da China
Rahotonni sun ce a shekarar 2018 aka fara sa hannu a wannan yarjejeniya ganin yadda ake fama da karancin kudin ketare a CBN.
A lokacin da ake saida Dalar Amurka a kan N305 a Najeriya, an ware Dala biliyan 2.5 wanda ya kai Yuan biliyan 15 da Naira biliyan 720.
Premium Times ta ce Sin ta na cikin kasashen da suka fi kowane alakar kasuwanci da Najeriya.
Alakar kasuwancin China da Najeriya
Kasar ta yi fice wajen saye da sayar da kayan amfanin gona, mai, kayan wutar lantarki, na’urori da kuma kayayyakin yin gini iri-iri.
Ana fata idan Najeriya ta rage dogara da Dala ko sauran kudin ketare wajen ciniki a kasuwannin duniya, Naira za ta kara kima.
Gwamnatocin Najeriya sun raba N3.1tr
Ana da labari cewa an samu Naira tiriliyan 3.14 amma an raba Naira tiriliyan 1.72 a kason FAAC a karshen watan Nuwamban 2024.
An raba kudin ne tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomin Najeriya a watan jiya kamar yadda aka saba al'ada.
Asali: Legit.ng
