'Tinubu ba Makiyinmu ba ne': Sanata kan Kudirin Haraji, Ya Fadi Gatan da Aka Yi wa Arewa

'Tinubu ba Makiyinmu ba ne': Sanata kan Kudirin Haraji, Ya Fadi Gatan da Aka Yi wa Arewa

  • Sanata Ahmed Wadada daga jihar Nasarawa ya karyata zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na neman kawo cikas ga Arewaci ta hanyar kudirin haraji
  • Sanata Wadada ya bayyana cewa ayyukan Tinubu kamar aikin titin Abuja-Kaduna-Kano suna nuna goyon bayansa ga Arewacin Najeriya
  • Wadada ya ce duk da karin haraji, Shugaba Tinubu ba ya da wata manufa ta cutar da yankin Arewa, yana mai kiran mutane su yi hakuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nassarawa - Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya musanta zargin cewa Bola Tinubu yana yakar Arewacin Najeriya ta hanyar gabatar da kudirin haraji.

Sanatan dan jam'iyyar SDP daga jihar Nasarawa ya ce ko kadan Tinubu ba shi da mummunan nufi kan Arewacin kasar.

Sanata a Arewa Ya kare matakin kudirin haraji a Najeriya
Sanata Ahmed Wadada ya kare Bola Tinubu kan kudirin haraji. Hoto: Senator Ahmed Wadada.
Asali: Facebook

'Tinubu ya yi wa Arewa gata' - Sanata

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

Wadada ya yi wannan jawabi ne yayin da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Asabar 28 ga watan Disambar 2024, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya ce manyan ayyukan gwamnatin Tinubu a yankin suna nuna tsayin dakan gwamnati wajen inganta Arewa.

A cewarsa, waɗannan ayyukan sun sabawa zargin cewa Shugaban yana cutar da Arewa ta hanyar haraji.

Sanata Wadada wanda shine shugaban kwamitin binciken asusun gwamnati na majalisar dattawa, ya ce fargabar mutane kan gyaran harajin ba su da tushe.

Sanata a Arewa Ya kare kudirin haraji

"Babu wani dan Arewa da zai ji tsoron haraji; mun dade muna biyan haraji kamar na dabbobi tun kafin wasu su fara, muna fahimtar cewa don cimma buri, dole a samu isassun kudade."
"Mai yunkurin cutar da Arewa ya san muna da hanyoyin kare kanmu, ban dogara da ra'ayin jama'a ba, amma ina duba lamarin ta mahanga mai ma'ana."

Kara karanta wannan

'Siyasa ce': An zargi Nijar da neman hada gaba mai tsanani tsakanin yan Arewa da Tinubu

- Sanata Wadada

Wadada ya kuma ce gwamnatin Tinubu ba ta da wata manufa ta cutar da kowace sassa ta Najeriya, amma duk wani abu sabo yana bukatar tuntuba mai kyau.

'Ban yi nadamar cire tallafi ba" - Tinubu

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce babu nadama kan cire tallafin man fetur a watan Mayu 2023 da ya yi a Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin ya kawo gasa a bangaren man fetur, inda farashin ya fara raguwa a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.