Bayan Kama Yan Uwansa, Turji Ya ba Gwamnati Umarni, Ya Fadi Abin da Zai Faru a 2025

Bayan Kama Yan Uwansa, Turji Ya ba Gwamnati Umarni, Ya Fadi Abin da Zai Faru a 2025

  • Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo inda yake gargadi ga hukumomi a jihar Sokoto
  • Dan ta'addan ya bukaci sake musu yan uwansu da ke hannun hukumomi ko kuma su fuskanci hare-hare a 2015
  • Wannan na zuwa ne baan wasu rahotanni sun tabbatar cewa an cafke wasu daga cikin mataimakan Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Hatsabibin dan bindiga, Bello Turji ya sake fitar da wani sabon bidiyo kan kama wasu yan uwansa.

Dan ta'addan ya gargadi hukumomi kan sako musu yan uwa da aka kama ko su fuskanci hare-hare.

Bello Turji ya gargadi hukumomi a sabon bidiyon da ya fitar
Bello Turji ya sha alwashin kai hare-hare a 2025 idan ba a sake yan uwansu ba. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Turji ya sake yin bidiyo kan ta'addaci

Wannan sako na kunshe a cikin wani faifan bidiyo da Malam Murtala Bello Asada ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Yadda aminin Turji ke tsula tsiyarsa, wasu a yankin Sokoto sun roki gwamnati alfarma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Bello Turji ya gargadi hukumomi kan sake musu yan uwansu ko kuma a fuskanci munanan hare-hare musamman a sabuwar shekarar 2025.

Dan ta'addan ya caccaki sojojin Najeriya kan yadda suke yada karairayi kan cewa suna yin nasara kansu a Arewacin Najeriya.

Gargadin Turji ga hukumomi kan kama yan uwansu

"Muna son tura sako ga al'ummar jihar Zamfara da Sokoto saboda wasu abubuawa da muke gani suke faruwa."
"Muna tunatar da al'ummar karamar hukumar Shinkafi kan wannan iftila'in da suke son jawo mana na kashe-kashen junanmu."
"Muna kira gare su kafin wannan sabuwar shekara ta 2025 su sake mana yan uwanmu da suke hannunsu idan ba haka ba muna sanar musu cewa shekara ce da zamu bude ta da yake-yake."

- Bello Turji

Bello Turji ya magantu bayan kama amininsa

Kun ji cewa bayan jami'an tsaro sun yi nasarar cafke dan ta'adda, Bago Wurgi, shugaban yan bindiga, Bello Turji ya yi martani.

Kara karanta wannan

'Ku koyi rayuwa a haka': Tinubu ya ba yan Najeriya satar amsa kan tsadar wutar lantarki

Bello Turji ya yi barazanar daukar munanan matakai na kai hare-hare a wasu yankunan da ke Sokoto da Zamfara.

Rahotanni sun ce Turji zai iya yin komai tun daga ba da dukiyarsa zuwa kai hare-hare idan ba a sako Wurgi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.