An Kona Makarantar Kandahar a Bauchi: Rigima Ta Kaure Tsakanin Matasa da Ƴan CJTF

An Kona Makarantar Kandahar a Bauchi: Rigima Ta Kaure Tsakanin Matasa da Ƴan CJTF

  • 'Yan sanda sun cafke wasu mutum 15 da ake zargi da kone makarantar firamare ta Kandahar da ke a kwaryar jihar Bauchi
  • SP Ahmed Wakil ya ce rikici ya barke tsakanin matasa da mambobin CJTF, wanda ya kai ga kona makaranta da ofishin CJTF
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Mohammed, ya umurci sashen bincike da su gano musabbabin wannan danyen aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - 'Yan sanda a jihar Bauchi sun kama mutum 15 da ake zargi da hannu a kone wani bangare na makarantar firamare a Kandahar, jihar Bauchi.

Rahotanni sun ce an kona makarantar ne bayan wata arangama tsakanin matasan Bauchi da jami'an Civilian Joint Task Force (CJTF) a yankin.

Rundunar 'yan sanda ta yi magana yyain da aka fafata tsakanin matasa da 'yan CJTF a Bauchi
Bauchi: An kone makaranta da ofishin CJTF a Bauchi, 'yan sanda sun kama mutum 15. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An kona makaranta da ofishin CJTF

Haka kuma, ofishin CJTF da ke kusa da makarantar shi ma an kona shi yayin rikicin, kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya bayyana.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da wata tankar mai ta tarwatse ana cikin jimamin rasa rayuka a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

SP Wakil ya ce yayin rikicin, jami'an CJTF sun yi arangama da matasan, inda daya daga cikin su, Saidu Musa, mai shekara 22, ya ji rauni.

Bauchi: An garzaya da jami'in CJTF asibiti

Musa ya samu harbin bindiga a kirjinsa daga wata bindiga da aka kera a gida, inda aka garzaya da shi asibitin kwararru na Bauchi don jinya.

Kakakin ya yi kira ga jama'ar Bauchi da su guji daukar doka a hannunsu kuma su kai rahoton duk wata matsala ga hukumomin da ya dace.

Wakil ya ce kwamishinan ‘yan sanda na Bauchi, Auwal Mohammed, ya umarci sashen binciken manyan laifuka na jihar da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Matasa sun farmaki dan majalisar Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun yiwa dan majalisarsu ature tare da farmakarsa a lokacin da ya kai ta'aziyyar rasuwar sarkin Ningi.

An ce dan majalisar Ningi/Warji a majalisar wakilai, Hon. Adamu Hashimu Ranga ya sha dakyar a hannun matasan, duk da jami'ai sun yi harbin bindiga a sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.