Sojojin Najeriya Sun Cafke 'Yan Tawayen Kasar Waje da Suka Shigo Jihar Arewa
- Sojoji sun kama 'yan tawaye hudu daga Kamaru a Taraba bisa zargin safarar makamai tare da hadin gwiwar wasu 'yan Najeriya
- An rahoto cewa 'yan tawayen na Ambazonia sun bayar da bayanai na safarar makaman da suke yi da kayan da suke karba
- Sojoji sun kuma kwato bututun mai guda 30 mallakar NNPCL a Wukari yayin wani atisayen hadin gwiwa da jami'an NSCDC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Rundunar sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) ta kama 'yan tawayen Ambazonia hudu 'yan asalin Jamhuriyar Kamaru da suka shigo Najeriya.
An cafke 'yan tawayen ne a wani otel da ke karamar hukumar Takum, jihar Taraba bayan samun sahihin bayanan sirri a ranar 18 ga Disamba, 2024.
An kama 'yan tawayen Kamaru a Taraba
Kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa suna cikin masu safarar makamai daga Kamaru zuwa Najeriya inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda ake zargin sun bayyana cewa suna cinikayyar makaman ne da garin 'Cocoa' tare da hadin gwiwar wasu ‘yan Najeriya.
An gano wayoyi hannu hudu a hannun 'yan tawayen Kamaru kuma suna tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Taraba: Sojoji sun kwato kadarorin NNPCL
A wani samamen na daban, sojoji sun kama wata mota mai lambar WKR 66 BB Taraba a Natilde da ke Wukari, dauke da bututun man fetur guda 19.
Bututun man fetur din mallakar kamfanin NNPCL ne, kuma an gano karin guda 11 yayin hadin gwiwar sojoji da NSCDC, wanda ya kawo jimillar su 30.
An mika dukkanin kayan da aka kwato ga hukumar NSCDC reshen Wukari domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.
Sojoji sun kama masu safarar makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya sun cafke wasu masu safarar makamai biyu a jihar Filato suna shirin sayen bindigar AK-47.
Rundunar ta shaida cewa mutanen biyu sun jima suna safarar makamai tare da gudanar da ayyukan ta'addanci a Filato inda ake farautar sauran 'yan uwansu.
Asali: Legit.ng