Fitaccen Mawaki Ado Gwanja Zai Sake Rikita Arewa, Ya Saki Sabon Kundin Wakoki 18
- Fitaccen mawaki Ado Isa Gwanja daga Arewa ya saki sabon kundin wakokinsa mai taken 'Dama Nine' a ranar 20 ga Disamba
- Kundin ya ƙunshi sababbin wakoki 18 da ake iya sauraron su a dandalolin sauraron wakoki na intanet, kamar yadda bincike ya nuna
- Masoyansa sun jima suna jiran wannan kundin, wanda ya kunshi wakoki kamar Cikina, Dama Nine, da Son Zuciya da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitaccen mawakin Hausa daga Arewacin Najeriya, Ado Isa Gwanja, ya saki sabon kundin wakokinsa da ya yiwa taken: "Dama Nine".
Tun da aka shigo shekarar 2024, mawaki Ado Gwanja bai saki wani kundin wakoki ba har sai da karshen shekarar ya zo.
Ado Gwanja ya saki sabon kundin wakoki
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Ado Gwanja ya ce kundin wakokinsa mai taken 'Dama Nine' ya fita a ranar 20 ga Disamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta gano cewa yanzu haka mutane sun fara sauraron wakokin da ke cikin wannan kudi a kafofin sauraron wakoki kamar Audio Mack, Aple Music, YouTube da sauransu.
Masoyan wakokin Ado Gwanja sun dade suna tsumayin fitowar wannan kundin na 'Dama Nine' kasancewar ya dade bai saki wani kundi ba.
Wakoki 18 da ke cikin kundin wakokin Gwanja
Ado Gwanja ya sanya sababbin wakoki 18 a cikin kundin 'Dama Nine' da nufin kayatar da masu sauraron wakokinsa.
Legit Hausa ta tattaro jerin kundin wakokin, duba a kasa:
- Cikina
- Duniya labari
- Jirgin yawo
- Dama Nine
- Ba madara ba
- Son zuciya
- Congratulation Amarya
- Aniyar kowa
- Haye haye
- In zo
- Muna nan
- Rigaa
- Madara
- So ne
- Zaman duniya
- I like the way
- Mata ku fito
- Gidan duniya
Yanzu masoya sun fara tsumayin lokacin da mawaki Gwanja zai fara daukar bidiyon wakokin cikin wannan kundi.
An yi bikin radin sunan diyar Ado Gwanja
A wani labarin, mun ruwaito cewa an gudanar da shagalin bikin radin sunan diyar fitaccen mawakin Hausa, Ado Isa Gwanja tare da matarsa Maimunatu.
Yayin da aka radawa yarinyar suna Asiya Ado Gwanja an ga wasu zafafan hotunan kayataccen bikin radin sunan da Gwanja da Maimunatu suka yi.
Asali: Legit.ng