Farashin Shinkafa Ya Karye daga N84000, An Fadi Kasuwar da Ake Samunta da Sauki

Farashin Shinkafa Ya Karye daga N84000, An Fadi Kasuwar da Ake Samunta da Sauki

  • Farashin shinkafar gida mai tsafta ya ragu da kashi 10 a jihar Enugu, inda yanzu buhu mai nauyin kilo 50 ya koma kasa da N78,000
  • 'Yan kasuwar awo sun shawarci al'umma da su yi amfani da wannan damar wajen sayen shinkafar da yawa kafin ta kara kudi
  • Jama’a na jin dadin farashin da ya ragu saboda hakan zai ba su damar yin hidimar bukukuwan karshen shekara a wadace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Farashin shinkafar gida mnarar tsakuwa ya ragu da kashi 6 zuwa 10 a kasuwannin Enugu, wanda ya sa mutane suka fara dafifin saye.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye shiryen bukukuwan Kirsimeti, da na karshe da kuma farkon shekara a Najeriya.

'Yan kasuwa sun yi magana yayin da farashin shinkafa ya ragu a Enugu
Farashin shinkafar gida ya ragu a kasuwannin Enugu. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Enugu: Farashin shinkafar gida ya ragu

Kamfanin dillancin Labarai na Najeriya ya rahoto cewa, 'yan kasuwa sun alakanta faduwar farashin da zuwan lokacin girbin shinkafar ta gida.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na fuskantar matsala daga Arewa, za a raba shi da kujerarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata ‘yar kasuwa a kasuwar Ogbete, Rose Nwakwo, ta ce farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yanzu ya koma N78,000, daga N84,000 da ake sayarwa a Nuwamba.

Wani dillali a kasuwar Garki, Chidi Orji, ya ce kwano daya mai cin lita biyar yanzu ya sauka zuwa N6,500, daga N7,500.

Orji ya bukaci jama’a da su sayi abin da za su iya kafin farashin ya sake tashi.

'Yar kasuwa ta fadi shinkafa mai arha

Jaridar The Punch ta rahoto cewa masu sayar da shinkafa da kwano ko mudu na tara kaya domin amfanin lokacin bukukuwan karshen shekara.

Wata ‘yar kasuwa a kasuwar Mayor, Eunice Madu, ta ce tana tara buhunan shinkafar gida don cin kasuwar bukukuwan Kirsimeti.

“Gaskiya muna sayar da duk shinkafar gida mai tsafta da aka fi sani da ‘Abakaliki rice’ kafin lokacin bukukuwa,” in ji Madu.

Wani mai sayen shinkafa, Edwin Okoh, ya ce ya ji dadi da farashin ya ragu, yana mai cewa albashinsa zai iya sayen fiye da buhu daya yanzu.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Wani ciyaman ya bi sahun gwamnoni, ya gabatar da kasafin biliyoyi a 2025

Shinkafa ta koma N52,000 a Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa farashin shinkafa mai nauyin kilo 50 ya karye daga N60,000 zuwa tsakanin N52,000 da N54,000 a kasuwannin jihar Kwara.

Wasu 'yan kasuwa sun shaida cewa akwai yiwuwar farashin shinkafar ya sauka har zuwa kasa da N40,000 amma zai danganta ne da samuwarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.