Lauyoyi Sun Gano Kuskuren DSS a Tsare Shugaban Miyetti Allah, An Shigar da Kara

Lauyoyi Sun Gano Kuskuren DSS a Tsare Shugaban Miyetti Allah, An Shigar da Kara

  • Shugaban 'yan Miyetti Allah, Bello Bodejo, ya shigar da kara don neman kotu ta ba da umarnin a sakin shi daga hannun DSS
  • Matar Bodejo, ta bayyana cewa an tsare mijinta ba bisa ka’ida ba bayan rikici tsakanin Fulani da wani tsohon sojan ruwa
  • Lauyoyi sun ce tsare Bodejo ba tare da gurfanarwa ba ya saba dokar kasa, kuma yana bukatar ganin likita game da lafiyarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo, ya yi karar Antoni Janar na tarayya da shugaban hukumar DSS kan tsare shi ba tare da gurfanarwa ba.

A cikin wata bukata da aka shigar a kotu, lauyoyinsa suna neman kotun ta ba da umarnin sakin Bodejo daga hannun DSS inda aka tsare shi.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Lauyoyi da matar shugaban Miyetti Allah sun yi maagana kan tsare Bodejo a hannun DSS
Shugaban Miyetti Allah ya aika bukata gaban kotu bayan ci gaba da tsare shi a hannun DSS. Hoto: Bello Bodejo
Asali: Twitter

Shugaban Miyetti Allah ya yi karar AGF, DSS

Bodejo ya bukaci kotu ta ba shi damar neman "habeas corpus subjiciendum" don tilasta DSS gabatar da shi a gaban kotu da bayyana dalilin tsare shi, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Habeas corpus subjiciendum kalmar shari'a ce da ke nufin a tilasta hukumomi su gabatar da wanda ake tsarewa gaban kotu don tabbatar da halaccin tsare shi.

A ranar 9 ga Disamba, iyalan Bodejo suka ce an kama shi a Nasarawa kuma aka tsare shi ba tare da an gurfanar da shi gaban wata kotu ba har zuwa yanzu.

Lauyoyi sun ga kuskuren tsare Bodejo

Lauyan Bodejo ya ce sojoji sun tsare wanda yake karewa a hannun DIA har zuwa ranar 18 ga Disamba ba tare da gurfanar da shi ba.

Daga nan ne kuma aka ce an mika Bodejo daga DIA zuwa DSS a Abuja ranar 19 ga Disamba, inda ake tsare da shi har yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na fuskantar matsala daga Arewa, za a raba shi da kujerarsa

Hauwa, matar Bodejo, ta bayyana cewa an kama Bello Bodejo bayan rikici tsakanin makiyaya da wani tsohon jami’in sojan ruwa a Shuwari, Nasarawa.

Matar Bodejo ta koka kan tsare mijinta

Ta ce tsohon jami’in ya harbe dabbobi guda hudu, lamarin da ya jawo rigima a tsakaninsu har ta kai ga yi wa sojan rauni, amma an kai shi asibiti tare da biyan kudin maganinsa.

Hauwa ta ce daga bisani tsohon sojan ya hada kai da sojoji, suka kama wasu Fulani, suka kwace shanu 400 sannan kuma suka tsare Bodejo saboda zai shiga tsakani.

Ta kara da cewa an hana mijinta ganin likita ko amfani da magungunsa, kuma bai samu damar kare kansa ba tun lokacin da aka kama shi.

Majalisa ta bukaci sakin Bello Bodejo

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta gayyaci shugabannin sojoji da na tsaro kan kama shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo, ba tare da bin ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya ce bayan Wike ya kwace filinsa da na wasu manya a Abuja

Majalisar ta kuma umarci sojoji da su saki Bodejo daga tsarewar da aka yi masa ba bisa ka’ida ba, tare da ba shi hakuri saboda keta hakkinsa na dan Adam.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.