Ministan Tinubu Ya Kwace Filayen Buhari, Uba Sani da Wasu Manyan Mutane a Abuja
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kwace filaye 762 a Maitama saboda rashin biyan kuɗin takardun mallakar filayen (C-of-O)
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan Kaduna, Uba Sani na daga cikin wadanda Wike ya kwacewa filaye
- Hukumar FCTA ta bai wa masu mallakar filaye 614 wa’adin makonni biyu su biya bashin kuɗi da ake binsu ko su rasa filayensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kwace filaye 762 a Maitama, Abuja, saboda rashin biyan kuɗin haraji na takardun mallakar fili (C-of-O).
A cewar sanarwar hukumar FCTA, waɗanda abin ya shafa sun gaza biyan kuɗin da ake buƙata don tabbatar da mallakar filayensu a yankin.
Wike ya kwacewa Buhari da wasu filaye
Wadanda suka rasa filayensu sun hada da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
hukumar FCTA ta kuma yi barazanar kwace filaye 614 idan masu su suka gaza biyan bashin kuɗin filayen a cikin makonni biyu.
Dokar amfani da filaye ta 1978 ta bai wa minista ikon kwace filaye saboda rashin biyan kuɗin haraji ko keta dokar raba filaye.
Wadanda Wike ya kwacewa filaye a Abuja
Premium Times ta lissafa sunayen waɗanda aka kwace filayensu da suka haɗa da gidauniyar kudi ta Muhammadu Buhari, da wasu manyan shugabanni.
Shugabannin sun haɗa da shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da gwamnan Kaduna, Uba Sani.
Wasu tsofaffin 'yan majalisa da aka ambata su ne Tahir Monguno, Teslim Folarin da Andy Uba, sannan tsohon alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen na cikinsu.
Abuja: Manufar kwace filayen mutane 762
Nyesome Wike ya ce yana da niyyar tabbatar da doka a tsarin kula da filaye a Abuja tun bayan karɓar aiki a watan Agusta 2023.
Yayin wata ganawa, ya ce:
“Duk lokacin da aka yanke wani hukunci bisa doron gaskiya, wasu za su ji daɗi, wasu kuma ba za su ji daɗi ba.”
Wannan mataki na hukumar FCTA na da nufin tabbatar da tsari da gaskiya a kula da filaye a babban birnin tarayya Abuja.
Wike ya kwace filayen Peter Obi, BUA
A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya kwace filayen wasu manyan 'yan Najeriya ciki har da Peter Obi a Abuja.
Wike ya ce ya kwace filayen mutanen da suka hada da Obi, Abdul Samad Rabiu BUA da sauransu saboda sun ki bunkasa su duk da sanarwar da aka yi masu.
Asali: Legit.ng