Magana Ta Kare, Kotun Koli Ta Yi Hukuncin Karshe kan Shari'ar Neman Tsige Tinubu
- A ranar 16 ga Disamba, Kotun Koli ta yi watsi da karar da ke neman korar Bola Tinubu daga mukaminsa na shugaban kasa
- Kotun, ta ci tarar Cif Ambrose Owuru, wanda ya shigar da karar Naira miliyan biyar, tare da hana shi shigar da sabuwar karar
- Ambrose ya yi zargin cewa Tinubu jami’in CIA ne kuma ya nemi kotun ta kore shi bisa dalilan shari’o’in da suka shafi kwayoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin din nan, 16 ga watan Disambar 2024, Kotun Koli ta yi watsi da karar da ke neman korar Shugaba Bola Tinubu daga mukaminsa.
Kotun kolin, a wani mataki na bai daya da wasu alkalai biyar suka yanke, ta ci tarar Naira miliyan biyar ga wanda ya shigar da kara, Cif Ambrose Owuru.
Kotun koli ta kori karar tsige Bola Tinubu
Cif Ambrose Owuru shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) a zaben 2019 da ya gabata, a cewar rahoton Vangaurd.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin wanda mai shari’a Uwani Musa Abba-Aji ya jagoranta, ya gargadi bangaren magatakardar kotun koli da kada ya sake karbar duk wata kara daga Cif Ambrose.
A karar da ya shigar, Cif Ambrose ya shaidawa kotun kolin cewa Tinubu jami'in hukumar CIA da ke Amurka ne, don haka bai cancanci zama shugaban kasa ba.
Dalilan Ambrose na neman korar Tinubu
Hakazalika mai shigar da karar ya bukaci kotun ta kori Tinubu a kan batun cewa ya sallama $460,000 ga gwamnatin Amurka a wata shari’ar da ta shafi harkar kwayoyi.
Ya kuma roki kotun koli da ta yi amfani da sashe na 157 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ta kori Tinubu saboda kasancewarsa karkashin ikon hukumomin kasashen waje.
Punch ta rahoto cewa ko bayan zaben shugaban kasa na 2023, Cif Owuru ya garzaya kotun daukaka kara da ta dakatar da rantsar da Tinubu, koken da kotun ta ki karba.
Ambrose ya gagara nasara a tsige Buhari
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da bukatar Cif Ambrose Owuru na korar Muhammadu Buhari.
Cif Ambrose ya kalubalanci nasarar Buhari a zaben 2019 da ya lashe, inda ya roki kotun da ta kori shugaban tare da ayyana shi a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng