Magidanta Na Tserewa Suna Barin 'Ya 'Ya da Matansu a Gombe, NHRC Ta Gano Dalili

Magidanta Na Tserewa Suna Barin 'Ya 'Ya da Matansu a Gombe, NHRC Ta Gano Dalili

  • Hukumar NHRC ta karɓi rahoton cin zarafin ɗan adam 339 a Gombe, mafi yawanci yana shafar rashin kulawar maza ga iyalinsu
  • Malam Ali Alola-Alfinti ya ce wayar da kan jama’a kan cin zarafin haƙƙin ɗan adam ya sa rahotannin suka karu a jihar Gombe
  • Cin amanar iyaye ya kai kashi 50 na rahotannin, wanda ya shafi yadda maza kan tsallake su bar iyali ba abinci, tufafi ko muhalli

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC) ta ce ta karɓi rahoton zargin cin zarafin hakkin ɗan adam 339 a jihar Gombe a 2024.

NHRC ta ce mafi yawancin rahotannin sun shafi rashin kulawar iyaye, inda iyaye maza ke guduwa su bar matansu da ‘ya’yansu saboda matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

"Mutane za su ji daɗi," An buƙaci Tinubu ya dawo da farashin fetur N300 na watanni 2

Hukumar NHRC ta yi magana kan karuwar rahotannin cin zarafin dan Adam a Gombe
Hukumar NHRC ta samu rahotanni 339 na cin zarafin dan Adam a jihar Gombe.
Source: Original

Kakakin hukumar, Malam Ali Alola-Alfinti, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Gombe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wayar da kai kan cin zarafin dan Adam

Malam Ali ya ce yawaitar rahotannin na da alaƙa da wayar da kan jama’a kan cin zarafin ɗan Adam da ake ci gaba da gudanarwa a jihar.

A cewarsa, hukumar ta haɗa kai da kungiyoyin farar hula, kafafen yaɗa labarai, shugabannin addinai da al’umma don ilimantar da jama’a kan muhimmancin fadar gaskiya.

“Yanzu muna samun ƙarin rahotanni daga wadanda abin ya shafa. Wannan yana da kyau don cigaban yaƙi da cin zarafin hakkin ɗan adam,” inji kakakin NHRC.

Magidanta ta tserewa su bar iyalansu

Ya kara da cewa shiru na kasancewa babban kalubale a yaƙin kare hakkin ɗan adam, saboda ba za a iya kare hakkin mutum ba idan bai bayar da rahoto ba.

Tribune ta rahoto hukumar ta ce rahotannin 339 da aka samu suna da alaƙa da goyon bayan masu ruwa da tsaki da aka samu wajen wayar da kan al’umma.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fahimci halin da ake ciki, ta taso bankin CBN a gaba kan takardun kuɗi

Cin amanar iyaye yana da yawa a cikin rahotanni, inda ya kai kusan kashi 50, ciki har da tsallakewar magidanta su bar iyalansu ba tare da abinci ko muhalli ba.

Hukumar ta ƙara yawan tarurruka don magance matsalar, tana kuma wayar da kan maza kan muhimmancin kula da iyalansu da haƙƙin iyaye akan yara.

Matan aure sun lakadawa mazajensu duka

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Legas ta bayyana cewa kimanin maza 70 sun kai rahoton cewa matayensu sun lakada masu dukan tsiya a shekara guda.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne yayin da ma'aikatar harkokin mata, karkashin Bolaji Cecilia-Dada, ta karɓi korafe-korafen cin zarafin mata da maza guda 662.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com