Kotu Ta Ceci Facebook, Ta Hana Gwamnati Ta Laftawa Kamfanin Tarar Naira Biliyan 60

Kotu Ta Ceci Facebook, Ta Hana Gwamnati Ta Laftawa Kamfanin Tarar Naira Biliyan 60

  • An saurari karar da lauyan Facebook ya shigar a wata babban kotun tarayya da ke zama a garin Legas
  • Facebook ya kalubalanci tarar kudin da aka ci shi da sunan ya sabawa ka’idojin aiki da talla a Najeriya
  • Yellim Bogoro ya gamsu da duka bukatun Mofesomo Tayo-Oyetibo, ya umarci ARCON ta dakata da tarar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Legas ta saurari shari’ar da Facebook yake yi da gwamnatin Najeriya.

Babban kotun tarayyar ta soma takawa hukumar ARCON mai kula harkokin talla burki wajen yabawa Facebook tara.

Facebook
Gwamnati ta yabawa Facebook tarar N60bn a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shari'ar Facebook da hukumar AMCON

The Cable ta ce hukumar ARCON ta na zargin Facebook da sabawa ka’idoji kasar, don haka ake neman su biya N50bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a Yellim Bogoro da ya saurari karar a ranar Alhamis ya bukaci ARCON ta dakata tukuna daga karbar tarar kudin.

Kara karanta wannan

A karshe, Jonathan ya samu damar gwabzawa da Tinubu a 2027

Vanguard ta ce Yellim Bogoro ya yi zama a kan shari’ar mai lamba FHC/L/CS/2205/2024.

Mofesomo Tayo-Oyetibo wanda kwarerren lauya ne da ya yi karatu a Birtaniya shi ne lauyan da ya tsayawa Facebook.

Facebook sun fara samu sauki a kotu

Bayan sauraron karar da aka shigar, Alkalin ya ce ya gamsu a dakatar da cin tarar.

Alkalin ya bayyana cewa ya gamsu da bukatar da Mofesomo Tayo-Oyetibo ya shigar a madadin shahararren dandalin.

Hukuncin yana nufin ARCON ko jami’anta ko wasu wakilanta ba su isa su karbi wannan tara da aka bisa zargin saba doka.

Bayan ya gama yin hukunci, sai ya daga karar zuwa ranar 20 ga watan Fubrairu 2025, hakan yana nufin sai badi za a kotu kotu.

Mai kamfanin X ya mallaki $447bn

Dazu aka ji labari cewa a zamanin nan, ba a taba samun labarin mutumin da ya tara abin da ya kai Dala biliyan 400 ba sai kan Elon Musk.

Maganar da ake yi, mai kudin duniya watau Elon Musk ya na da dukiyar ta kusa kai Dala biliyan 450 watau Naira tiriliyan 690.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel