Ana Rigima kan Gyaran Haraji, Tinubu Ya Sanya Ranar da Zai Gabatar da Kasafin 2025
- Sanata Godswill Akpabio ya sanar da ranar da shugaba Bola Tinubu zai gabatar da kasafin shekarar 2025 ga majalisar tarayya
- A zaman majalisar dattawa na ranar Alhamis, Sanata Akpabio ya ce Tinubu zai gabatar da kasafin ne a Talatar mako mai zuwa
- Shugaban majalisar ya ce sanatoci za su fara ganawa a zauren majalisar kafin su je majalisar wakilai domin taron hadin guiwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya ranar da zai gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2025 ga majalisar tarayya.
A ranar 14 ga watan Nuwamba ne shugaban kasar ya sanar da kudurinsa na gabatar da Naira tiriliyan 48 a matsayin kasafin na 2025.
Bola Tinubu zai gabatar da kasafin 2025
Rahoton jaridar The Nation na yau Alhamis, 12 ga Disamba ya nuna cewa Tinubu zai gabatar da kasafin gaban majalisa a mako mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce majalisar wakilai da ta dattawa za su hade waje daya a ranar Talatar mako mai zuwa domin karbar daftarin kasafin daga Shugaba Tinubu.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.
Akpabio ya ce sanatoci za su fara haduwa a zauren majalisar dattawa kafin su wuce zuwa zauren majalisar wakilai domin taron hadaka.
'Yan Najeriya sun yi martani kan batun kasafin kudi
Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin 'yan Najeriya kan kasafin da shugaban kasar zai gabatar.
"Muna fatan ba za mu ji labarin cushe a kasafin wannan shekarar ba."
"Me ya yi da kasafin 2024 saboda ban ga wani bambanci ba."
"Da fatan ya haddace adadin kudin da ke cikin kasafin. Ba ma son a maimaita abin da ya faru a jihar Edo."
"A wannan shekarar kadai, an samu karin kasafi har guda hudu."
Kasafin 2025: Tinubu zai ba tsaro fifiko a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa ofishin kasafin gwamnatin tarayya ya shaida cewa shugaba Bola Tinubu zai ba fannin tsaro fifiko a kasafin 2025.
Daraktan ofishin kasafin tarayyar, Tanimu Yakubu ya ce 'yan Najeriya za su gamsu da abin da ke kunshe a kundin kasafin shekarar mai zuwa duk da tarin kalubale.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng