'Allah Ya Isa': Yaron Sarki Sanusi II kan Rigimar Sarauta, Ya Tuno Fadakarwar Mahaifinsa
- Dan Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuwa kan yadda 'makiya; ke neman batawa mahaifinsa suna
- Adam Lamido Sanusi ya ce duk wani kulli na mahassada ko masu sharri ba zai sauya abin da Allah SWT ya nufa ba
- Wannan martani na zuwa ne yayin da wani ya ci mutuncin Sarki Sanusi II wanda daga bisani ya nefi afuwar abin da ya aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake ta rigima kan sarauta a jihar Kano, yaron Sarki Muhammadu Sanusi II ya magantu kan wani hoto na mahaifinsa da aka wallafa.
Adam Lamido Sanusi ya koka kan yadda wasu makiya ke neman bayawa mahaifinsa da kuma iyalansu suna duk a kan rigimar sarauta.

Asali: Twitter
An wallafa hoton cin mutuncin Sarki Sanusi II

Kara karanta wannan
Tinubu ya ba Faransa damar kafa sansanin sojoji a Arewa? Rundunar tsaro ta magantu
Adam Lamido Sanusi ya bayyana haka ne a daren yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan martani na zuwa ne yayin da wani mai amfani da shafin X, Saifullahi Yahaya ya wallafa wani hoto na tsiraici da cin mutunci game da Sarki Sanusi II.
Daga bisani, bayan gane kuskurensa, matashin ya fito ya ba da hakuri inda yake neman tafiyar Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sai dai tuni ya goge hoton da ya wallafa inda wasu suka tabbatar da cewa an cafke shi kan zargin cin mutunci.
Dan Sanusi II ya magantu kan rigimar sarauta
Matashin ya ja Allah ya isa kan abubuwan da ke faruwa musamman bayan wallafa hoton inda ya ce bai san mene aka wallafa ba kuma bai son ya sani.
"Ban san abin da aka wallafa ba, kuma ba na sha'awar sani, mahaifina ya sha fada mana cewa Allah zai isar masa kan dukkan makiyansa da masu yi masa sharri."
"Komai abin da suka yi masa ba zai iya canza abin da Allah ya kaddara ba."
"Saboda haka, a madadin iyali babu abin da za mu ce kawa sai Allah ya isa."
- Adam Lamido Sanusi
Dan Sanusi ya tabo Amini Ado Bayero
Kun ji cewa 'dan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi martani bayan Aminu Ado Bayero ya sauka a fadar Nasarawa.
Ashraf Sanusi Lamido ya bayyana cewa masarautar Nasarawa tana karkashin ta Kano ce kamar yadda kowa ya sani.
Wannan martani nashi na zuwa ne bayan mahaifinsa, Muhammadu Sanusi II ya dauki lemar sarauta wanda ke tabbatar da mayar da shi karagar mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng