Wani Abin Fashewa da Ake Zargin 'Bam' ne Ya Tarwatse a Zamfara, Mutane Sun Mutu

Wani Abin Fashewa da Ake Zargin 'Bam' ne Ya Tarwatse a Zamfara, Mutane Sun Mutu

  • Wata motar haya dauke da fasinjoji ta taka wani abu da ake zargin 'bam' ne wanda ya jawo ta tarwatse tare da ajalin mutane 12
  • Wannan ne karo na biyu a mako guda da abin fashewa ta tashi a kan hanya, wanda ke barazana ga matafiya a yankin Dansadau
  • An nemi gwamnati da ta dauki matakin gaggawa yayin da aka yi kira ga jama'a da su yi taka tsantsan a lokacin tafiye-tafiyensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Wani abin fashewa da ake zargin 'bam' ne ya tarwatse a garin Yar Tasha, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.

Ana fargabar mutane 12 suka mutu sakamakon tarwatsewar 'bam' din, wanda ake ake zargin 'yan bindiga ne suka dasa shi a kan hanya.

Mazauna Zamfara sun koka yayin da aka sake samun tashin bam a Dansadau.
Ana fargabar mutane 12 sun mutu yayin da bam ya tashi a jihar zamfara. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bam ya hallaka mutane 12 a Zamfara

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

'Bam' din ta tashi ne da misalin ƙarfe 8 na safiyar Laraba lokacin da wata motar haya ta taka abin fashewar a kan hanyar Dansadau, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan shi ne karo na biyu cikin mako guda da abin fashewa ya tashi a kan hanyar Dansadau. A ranar Lahadi, wata motar haya ta fuskanci irin wannan waki'ar.

Wani mazaunin kauyen 'Yar Tasha ya ce motar kirar Gulf ta taka 'bam' din inda ta tarwatse nan take, wanda ya sa ake fargabar mutanen ciki sun mutu.

An roki gwamnati ta dauki matakin gaggawa

Jami’an tsaro, ciki har da sojoji da ‘yan sanda, sun isa wurin da abin fashewar ya tashi domin gudanar da binciken tsaro.

Wani mazaunin garin ya bayyana damuwa kan sabuwar dabarar ‘yan ta’adda na dasa bam a kan hanyoyin Dansadau, yana kira ga gwamnati da ta dauki mataki.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta cafke jami'anta saboda cin zarafin farar hula

Ya ce akwai bukatar jama'a su kasance masu lura yayin tafiye tafiye sannan gwamnati ta tabbatar an kawo ƙarshen wannan dabarar kafin ta yi muni sosai.

Abin fashewa ya tarwatse a Zamfara

Tun da fari, mun ruwaito cewa bam din da 'yan bindiga suka dasa a karkashin wata gada a karamar hukumar Maru, jihar Zamfara ya tartwatse a ranar Lahadi.

Mazauna Zamfara, musamman na yankin Dansadau sun ce ‘yan bindigar sun dasa bam din ne lokacin da suka je kai harin ramuwar gayya a Unguwar Galadima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.