'Ya Yi Batanci ga Shugaban Bankin UBA': 'Yan Sanda Sun Cafke Fitaccen Lauya a Najeriya

'Ya Yi Batanci ga Shugaban Bankin UBA': 'Yan Sanda Sun Cafke Fitaccen Lauya a Najeriya

  • ‘Yan sandan Najeriya sun cafke fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Dele Farotimi kan zargin ɓata sunan Tony Elumelu
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore ya yi kira da a saki Farotimi, yana mai zargin wata makarkashiya a kamen
  • Sowore ya kuma ce ‘yan Najeriya ba za su amince da amfani da ‘yan sanda wajen biyan bukatun wasu daidaikun mutane ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - ‘Yan sandan Najeriya sun cafke wani fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Dele Farotimi kan zargin ɓata sunan shugaban bankin UBA, Tony Elumelu.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 3 ga watan Disambar 2024.

Omoyele Sowore ya yi magana yayin da 'yan sanda suka cafke fitaccen lauya
'Yan sanda sun cafke fitaccen lauya kan zargin bata sunan shugaban bankin UBA. Hoto: @PoliceNG, @DeleFarotimi
Asali: Twitter

'Yan sanda sun cafke fitaccen lauya

Omoyele Sowore ya wallafa a shafinsa na X cewa Tony Elumelu ya shigar da ƙorafi kan Farotimi bisa zargin ɓata masa suna.

Kara karanta wannan

Hayaniya ta ɓarke a Majalisar Wakilai kan ƙudirin sauya fasalin harajin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yanzu nake samun labarin cewa ‘yan sanda sun kama Dele Farotimi bayan karar da Tony OElumelu na UBA ya shigar kan zargin Dele ya bata masa suna."

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya yi kira da a saki lauyan nan take, yana mai cewa ba za a yi amfani da ‘yan sanda don biyan bukatun wasu ba.

Sowore ya bukaci a sako Barista Farotimi

Sowore ya bayyana cewa:

"Ya zama wajibi mu ankarar da rundunar 'yan sandan Najeriya cewa ba za a ci gaba da amfani da rundunar wajen biyan bukatun wasu mutane ba.
"Mu 'yan Najeriya ba za mu ci gaba da zura idanu muna barin hakan tana faruwa ba."

Omoyele Sowore ya ce al’umma ba za su yi shiru ba idan ana amfani da hukumomi wajen biyan bukatun wasu daidakun mutane a kasar ba.

Ya kuma shawarci ‘yan sanda na Zone 2, jihar Legas da su saki Farotimi cikin gaggawa don kauce wa haifar da tashin tashina.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon ɗan Majalisar Tarayya, sun kashe ɗan sanda

Farotimi ya magantu kan ministocin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Dele Farotimi ya ce shugaba Bola Tinubu ba zai nada ministocin da za su yi wa Najeriya aiki ba.

A wata hira da aka yi da shi, Farotimi ya ce ‘ya ’yan jam’iyyar APC mai mulki ba su da kishin kasar nan a zuciyoyinsu kuma ministocin da za a zaba ba za su gyara kasar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.