"Ƴan Najeriya na Rayuwar Ƙarya": Tinubu Ya Fadi Wani Dalili na Cire Tallafin Fetur

"Ƴan Najeriya na Rayuwar Ƙarya": Tinubu Ya Fadi Wani Dalili na Cire Tallafin Fetur

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta daina biyan tallafin man fetur ne domin ceto Najeriya daga matsalar tattalin arziki
  • Ya bayyana cewa rayuwar da 'yan Najeriya da dama suka yi kafin cire tallafin man fetur 'ta karya ce' wadda zata haifar da matsala
  • Tinubu ya nuna damuwa kan yadda matasa ke tattara 'ya-nasu-'ya-nasu su bar kasar domin neman abin duniya a ƙasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Shugaba Bola Tinubu ya ce 'yan Najeriya na rayuwar karya kafin gwamnatinsa ta daina biyan kudin tallafin man fetur a shekarar 2023.

Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen bikin yaye daliban da suka kammala digiri a karo na 34 da 35 na jami'ar fasaha ta Akure.

Tinubu ya yi magana kan rayuwar da 'yan Najeriya ke yi kafin janye tallafin fetur
Tinubu ya koka kan yadda matasa ke tafiya ci rani kasar waje da batun janye tallafin fetur. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya ce cire tallafin man fetur da daidaita canjin kudade abu ne mai muhimmanci don ceto Najeriya daga durkushewar tattali, inji rahoton Channels.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi amfanin da cire tallafin man fetur ya yi wa Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan Najeriya na rayuwar karya" - Tinubu

Yayin da ya samu wakillcin shugaban jami'ar Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole, Tinubu ya bayyana matakan da ya dauka na yaki da matsalar tattalin kasar.

Shugaban ya ce:

“Mun karɓi ragamar shugabanci a lokacin da tattalin arzikinmu ke fuskantar matsala saboda bashin tallafin man fetur da na dalar Amurka.”
“Tallafin yana nufin taimakawa talakawa da inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Sai dai talakawa ne suka fi shan wahala daga wannan shiri.”
“Abin mamaki, rayuwar da muka dauka a matsayin mai kyau tana cike da ƙarya, wadda zata iya haifar da rushewar ƙasa idan ba a dauki matakin gaggawa ba.”

Shugaba Tinubu ya koka kan masu tafiya ci-rani

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban kasar ya yi bayanin dalilan da yasa dole ne a cire tallafin man fetur cikin sauri.

“Dole ne muka cire tallafin man fetur da na dalar Amurka domin ceto makomar yaranmu da kuma dawo da ƙasar daga durkushewa."

Kara karanta wannan

"Zan magance matsalolin Najeriya," Tinubu ya bayyana shirin da ya yiwa talakawa

- A cewar Tinubu

Shugaban ya nuna damuwa kan yadda ake samun yawaitar matasan Najeriya da ke barin kasar nan zuwa kasashen ketare neman 'abin duniya'.

“Da yawa daga cikin matasanmu sun zaɓi yin ƙaura zuwa kasashen ketare neman abin duniya maimakon su hada hannu domin ceto al’ummarsu daga kangin wahala."

- A cewar shugaban Najeriya

'Ya zama dole ne' - Tinubu kan cire tallafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya ce janye tallafin man fetur da ya yi a farkon hawansa mulk ya zama wajibi domin gyara tattalin arzikin kasar.

A cewar shugaban kasar, idan da bai daina biyan kudin tallafin ba, to da yanzu Najeriya ta fada cikin fatara wanda ba lallai ta iya fita a karamin lokaci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.