Tinubu Zai Wuce Afrika ta Kudu daga Faransa, An Fadi Lokacin da Zai Dawo Najeriya

Tinubu Zai Wuce Afrika ta Kudu daga Faransa, An Fadi Lokacin da Zai Dawo Najeriya

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron BNC na 11 tare da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a Cape Town
  • Taron zai mayar da hankali kan batutuwa daban-daban da suka shafi siyasa, tattalin arziki, tsaro, da kasuwanci tsakanin kasashen biyu
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa taron yana da muhimmanci yayin da ya zo a lokacin cika shekaru 25 na kafuwar BNC tun 1999

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

South Africa - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Faransa a ranar Litinin zuwa Afirka ta Kudu domin jagorantar taron kwamitin Najeriya da Afirka ta Kudu na BNC.

Bayan taron ministoci a ranar Litinin, 2 ga Disamba a Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu., an tsara babban taron shugabannin kasashen biyu a ranar Talata, 3 ga Disamba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abin da ya kamata Najeriya ta koya wajen Faransa

Bola tinubu
Tinubu zai tafi Afrika ta Kudu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook ta bayyana cewa shugabannin biyu za su tattauna muhimman abubuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da taron BNC zai tattauna

A yayin taron, kasashen za su tattauna kan abubuwa daban-daban da suka hada da siyasa, jakadanci, tsaro, masana’antu, kasuwanci, hakar ma’adinai da makamashi.

Shugabannin biyu za su yi nazari kan nasarorin da aka cimma tun bayan taron na karshe da aka yi a Abuja, tare da tsara hanyoyin da za su kara inganta dangantakar kasashen biyu.

Najeriya za ta yi yarjejeniya da Afrika ta Kudu

Daily Trust ta wallafa cewa wani muhimmin bangare na taron shi ne rattaba hannu kan yarjeniyoyi da takardun fahimtar juna.

An ruwaito cewa hakan zai tabbatar da kyakkyawar dangantaka da kuma inganta hadin kai tsakanin kasashen biyu.

Taron BNC zai cika shekaru 25 da kafuwa

Kara karanta wannan

Majalisa ta sa ranar taron kasa, za a zauna kan batun haraji, kananan hukumomi

Taron wannnar shekarar ya zo a lokacin cika shekaru 25 da kafuwar BNC, wanda ke nuna karfin zumunci da amana tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa Bola Tinubu zai samu rakiyar manyan jami'an gwamnati, kuma zai dawo Najeriya ne bayan taron.

Tazarcen Tinubu a 2027: AYCF ta yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa matasan Arewa sun bayyana cewa har yanzun ba a kai ga cimma matsaya kan marawa Tinubu baya ya yi tazarce ko akasin haka ba a 2027.

Shugaban ƙungiyar matasan (AYCF), Yerima Shettima ya ce duk wanda ya ce Arewa ta ɗauri ɗamarar yaƙar Bola Tinubu ƙarya yake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng