An Gurfanar da Surukin Buhari a Kotu, Ana Zargin Ya Karkatar da Kudin Jama'a
- Gimba Ya’u, tsohon shugaban FMBN, ya gurfana gaban kotu kan zargin karkatar da dala miliyan 65 na aikin gidaje a Abuja
- ICPC ta kuma tuhume shi tare da Bola Ogunsola da Tarry Rufus kan karkatar da kudaden lamunin banki na Naira biliyan 14
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta bayyanawa kotu dokokin da wadanda take kara suka take a tuhume tuhume biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar yaki da rashawa da dangoginsu (ICPC) ta gurfanar da Gimba Ya'u, surukin tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a kotu.
ICPC ta gurfanar da Gima Ya'u wanda ya kasance tsohon shugaban bankin lamunin gidaje na tarayya (FMBN) kan zargin karkatar da $65m na jama'a.
Gurfanar da surukin Buhari kan wawure kudi
A cewar wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar, hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta ce tana tuhumar Gimba Ya’u da laifuffukan safarar kudaden haram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ICPC ta zargi Gimba Ya'u da karkatar da kudaden da aka ware domin gina gidaje 962 a rukunin gidaje na Goodluck Jonathan Legacy City a Abuja.
An gurfanar da shi tare da Bola Ogunsola da Tarry Rufus a gaban Mai Shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya, Abuja.
Bola Ogunsola tsohon darakta ne a bankin FMBN yayin da shi kuma Tarry Rufus, ya kasance daraktan kafanin T-Brend Fortunes Nigeria Limite.
Tuhume-tuhumen rashin kammala aiki
ICPC ta gabatar da tuhume-tuhume biyar, tana zargin wadanda ta ke kara da karya dokokin kula da harkokin kasuwanci da safarar kudi ba bisa ka’ida ba.
An ce sun wawushe Naira biliyan 14 da suka karɓa daga bankin Ecobank a shekarar 2012 da zummar amfani da kudin wajen aiwatar da aikin gidajen.
Hukumar ta zargi surukin Buhari da ba da izinin biyan Naira biliyan 3.78 ga wani dan kwangila da aka san ba shi da ƙwarewar iya gudanar da aikin
Dokokin rashawa da surukin Buhari ya karya
ICPC ta shaidawa kotun cewa, saboda matsalar kwangilar aikin ya tsaya cak, wanda ya jawo wa bankin babban asara tare da karya dokar hukumar kula da kamfanoni.
Hukumar yaki da rashawar ta zargi wadanda take kara da aikata laifin da karya sashe na 68(1) na dokar hukumar kula da kamfanoni.
Wadanda ake karar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, kuma bayan bayanin da suka shigar, Mai shari’a Omotosho ya bayar da belinsu.
An dage shari’ar zuwa ranar 6 ga Fabrairu, 2025, don ci gaba da sauraron ƙarar.
Badakalar $65m: Auren Gimba Ya'u ya mutu
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a 2021 ta sanar da cewa auren Gimba Ya'u da diyar Buhari ya mutu.
A lokacin, fadar shugaban kasar ta ce Gimba Ya'u, wanda ICPC ke nema ruwa a jallo kan badakalar $65m ba surukin Buhari ba ne saboda wannan badakala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng