Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da angon Fatima Buhari

Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da angon Fatima Buhari

- Yarinyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biyu, Fatima Buhari na shirin aure a ranar Juma’a, 28 ga watan Oktoba.

- Zata auri wani mutumi mai suna Mallam Ya’u Gimba Kumo mai shekaru 57 a duniya

- Ga abubuwan ban sha’awa game da shi

Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da angon Fatima Buhari
Fatima Buhari da Mallam Kumo

Fatima Buhari ta kasance daya daga cikin yaran Buhari mata daga matarsa ta farko Safinatu Muhammadu Buhari kuma mijin da zata aura shine Mallam Ya’u Gimba Kumo mai shekaru 57 a duniya.

KU KARANTA KUMA: Ba’a Bukatar dakatar da shigo da abinci- Sarki Sanusi

An rigada an bada bayani game da angon nata wanda ya kasance tsohon manajan-darakta na bankin Mortage na tarayyar Najeriya, amma akwai wasu abubuwa guda biyar na ban sha’awa game da shi.

1. An haifi Mallam Ya’u Gimba Kumo a ranar 5 ga watan Nuwamba, na shekara 1959 a jihar Gwambe. Zai cika shekaru 57 a cikin watan Nuwamba mai zuwa, yana da shekaru 56 a yanzu.

2. Yana da takardan shaidan digiri a kan  harkan kasuwanci daga jami’ar Ahmadu Bello, Zaria wanda ya gama a shekara ta 1983. Yana kuma da digiri na biyu a kan harkan kasuwanci  (MBA) daga jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi wanda ya gama a shekara ta 1999.

Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da angon Fatima Buhari

3. An nada shi a matsayin Manajan-Darakta da kuma  shugaban bankin Mortgage na tarayyan Najeriya daga shekara ta 2010 zuwa 2014.

KU KARANTA KUMA: Kayi garambawul a hukumarka - Matasa ga Buhari

4. Yariga da yayi aure kuma yana da yara. Don bawai Fatima Buhari bace matarsa ta farko ko kuma matarsa kawai.

5. shi mutun ne mai himma wanda ya kasance mamba a kungiyoyi daban-daban. Wadannan kungiyoyi sun hada da: kungiyar Nigeria Institute of Certified Credit Administrators (AICCA), Nigeria institute of Management (NIM), Fellow of the Chartered Institute of Taxation of Nigeria (FCITN), Institute of Management Executive & Administration of Nigeria (MIMEA) da kuma Nigeria Institute of Certified Credit Administrators (AICCA).

Muna yiwa ma’auratan fatan alkahairi a gidan auransu.

Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da angon Fatima Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel