Da dumi-dumi: Buhari ya yi nadin sababbin mukamai, ya canza shugabannin FMBN

Da dumi-dumi: Buhari ya yi nadin sababbin mukamai, ya canza shugabannin FMBN

  • A yau Muhammadu Buhari ya nada wasu sababbin darektocin da za su rike bankin FMBN a Najeriya
  • Malam Garba Shehu ya bada sanarwar cewa Alhaji Hamman Madu ya zama sabon shugaban bankin
  • An tabbatar da nadin Ayodeji Gbeleyi a matsayin wanda zai shugabancin masu kula da aikin FMBN

Abuja - Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da wasu sauyi da aka samu a majalisar shugabannin da ke kula da aikin bankin FMBN na kasa.

Jaridar Daily Trust ta ce Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi a ranar Alhamis, 14 ga watan Afrilu 2022, yana mai bada wannan sanarwar a Abuja.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasar watau Garba Shehu ya bayyana cewa an yi wannan sauye-sauye ne domin kula da bankin yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi buda-baki da tawagar fastocin jihohi 19 na arewa

Hamman Madu wanda ya shafe sama da shekaru 30 a aikin banki, mai wakiltar yankin Arewa maso gabas shi ne babban darekta watau CEO na FMBN.

Sababbin darektocin da aka nada

Wadanda za su yi aiki tare da Madu a matsayin darektocinsa sun hada da Chukwuma Kingsley, Mustapha Lukman Olayiwola da kuma Asein Abimbola.

Haka zalika daga cikin wadanda aka zaba a matsayin manyan darektoci akwai Ejezie Sandra Nkechi da kuma wasu wakilai biyu da za su zo daga CBN.

Buhari
Muhammadu Buhari a Aso Villa Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Zubaida mai wakiltar Arewa maso yamma za ta kula da harkar tattalin arziki. Kingsley shi ne darekta na cigaban kasuwanci, zai wakilci Kudu maso kudu.

Lukman Olayiwola ya zama darekta mai kula da sha’anin bashi, shi ne mai wakiltar Kudu maso yamma, yayin da Nkechi ta ke wakiltar kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Daga kudu maso yamma akwai Asein Abimbola wanda ta zo daga ma’aikatar gidaje ta tarayya.

Ayodeji Ariyo Gbeleyi

PM News ta ce wa’adin dukkanin wadanda aka nada ya soma daga 13 ga watan Afrilun 2022, illa Ayodeji Ariyo Gbeleyi wanda tun Junairun 2022 aka nada shi.

Ayodeji Ariyo Gbeleyi shi ne shugaban majalisar da ke kula da harkokin bankin tarayyar.

Dangiwa ya bar Federal Mortgage Bank of Nigeria

A makon da ya wuce na mu ka kawo maku labari cewa Ahmed Musa Dangiwa ya kammala wa'adinsa a matsayin shugaban bankin bayan shekaru biyar.

Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) shi ne bankin tarayyan da ke ba ma’aikata damar mallakar gidajen kansu a Najeriya ta hanyar karbar bashi.

Ana tunanin Dangiwa zai nemi takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel