Yadda Malamai Suka Doki Matashiya Mai Bautar Ƙasa a Kwara, NYSC Ta Yi Magana
- Wasu malaman makaranta sun doki matashiya mai bautar ƙasa saboda ta gagara gaishe su yadda ya kamata
- Matashiyar da ba a bayyana sunanta ba ta gamu da tsautsayin ne a makarantar sakandare da ke Kulende a Ilorin da ke jihar Kwara
- Hukumar NYSC ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta sha alwashin daukar mataki kan cin zarafin matashiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kwara - An samu hayaniya a jihar Kwara bayan wasu malaman makaranta sun bugi matashiya mai bautar ƙasa.
Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024 a makarantar sakandare da ke Kulende a birnin Ilorin.
An zane matashiya mai bautar ƙasa a Kwara
Tribune ta ce malaman sun dauki matakin ne bayan matashiyar ba ta gaishe su yadda ya dace ba wanda hakan bai musu dadi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce matashiyar da ba a bayyana sunanta ba ta je makaranta domin karbar takardar tantancewa.
Wani shaidan gani da ido ya ce malamin ya kai mata farmaki inda ya yaga mata rigar hukumar NYSC da ke jikinta.
An soki malamai saboda cin zarafin 'yar NYSC
Daga bisani wata malama ta shiga fadan, ta zabgawa matashiyar mari nan take, Sahara Reporters ta ruwaito.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce har wasu ke bukatar a kaddamar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.
Lamarin ya sanya shakku a zukatan mutane kan yanayin kwarewa da kuma mutunta mutane a bangaren ilimi a kasar.
Hukumar NYSC za ta dauki mataki
Daraktan hulda da jama'a na hukumar NYSC a jihar, Morakinyo Oladipo ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Oladipo ya ce hukumar za ta dauki mataki kan cin zarafin matashiyar sannan ya ce an sanar da gwamnatin jihar abin da ya faru.
Ya ce a yanzu za a sauyawa matashiyar wurin aiki domin samun damar warkewa daga cin mutuncinta da aka yi.
Legit Hausa ya tattauna da matashi mai bautar ƙasa
Wani matashi mai bautar ƙasa a Gombe ya yi tsokaci kan wannan abin takaici da ya faru a Kwara.
Bashir Abubakar ya ce abin takaici ne yadda aka mayar da matasa masu bautar ƙasa a wasu wurare kamar almajirai.
Bashir ya ce ko kadan ba zai lamunci haka ba duk da ya san hukumar NYSC ta dauki mataki.
"Kwata-kwata hakan bai dace ba saboda ya zama cin zarafi kenan, ana bautar ƙasa saboda hadin kan al'umma ne."
"Idan haka ta faru da ni Allah ya kiyaye zan iya daukar mataki a karan kaina kafin NYSC da yi wani abu."
- Bashir Abubakar
Hukumar NYSC ta gyara dokar matan aure
Kun ji cewa Hukuma mai lura da matasa masu yi wa kasa hidima ta NYSC ta yi kwaskwarima ga wasu dokokinta da suka shafi matan aure.
A sabuwar dokar, an cire sharadin saka sunan miji ga matan aure kafin a tura su hidima a yankunan da mazajensu ke zama ko aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng