Abokin Sanusi II da Ya Taho daga Amurka Ya Ziyarce Shi a Fadar Sarkin Kano
- Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da wani abokinsa da da suka yi aiki tare a shekarun baya
- Bayan dawowarsa daga Amurka, Farfesa Kingsley Moghalu ya ziyarci sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a fadarsa
- Legit ta gano cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi aiki tare da Farfesa Kingsley Moghalu a babban bankin CBN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Masarautar Kano ta karbi baƙuncin babban abokin mai martaba Muhammadu Sanusi II.
Rahotanni sun nuna cewa Farfesa Kingsley Moghalu ya ziyarci Muhammadu Sanusi II ne bayan ya dawo Najeriya daga ketare.
Legit ta gano yadda ziyarar ta gudana ne a cikin wani sako da Kingsley Moghalu ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abokin Muhamadu Sanusi II ya ziyarce shi a Kano
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karbi baƙuncin abokin aikinsa, Farfesa Kingsley Moghalu.
Kingsley Moghalu ya kasance mataimakin gwamnan CBN yayin da Muhammadu Sanusi II ke jagorantar babban bankin.
Farfesa Moghalu ya taya sarki Sanusi II murnar dawowa kan karaga bayan sauke shi da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi.
"Bayan shafe shekaru bakwai a jami'ar Tufts a matsayin Farfesa, na dawo Najeriya.
Na kai ziyarar ban girma ga abokina, dan uwa na kuma shugabana a babban bankin Najeriya.
Na kasance mataimakin gwamnan bankin CBN yayin da Muhammadu Sanusi II ya kasance gwamna a bankin."
- Kingsley Moghalu
Tun a lokacin da Abba Kabir Yusuf ya dawo da Sarki Sanusi II Farfesa Kingsley Moghalu ya taya shi murna a kafafen sada zumunta.
Aminu Sanusi ya ziyarci Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa bayan nada Aminu Muhammadu Sanusi a matsayin Ciroman Kano, basaraken ya yi wata ziyara ta musamman a Jigawa.
Ciroman Kano watau DSP Aminu Muhammadu Sanusi ya gana da gwamnan Jigawa da sarkin Dutse a a ranar Laraba, 27 ga Nuwamba.
Aminu Sanusi ya samu rakiyar manyan mutanen fada da suka hada da Dokajin Kano, Dan Darman da Sarkin Yakin Kano da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng