Hajjin 2023: Hukumar Alhazai Za Ta Mayarwa Mahajjata 1,571 Miliyoyin Naira

Hajjin 2023: Hukumar Alhazai Za Ta Mayarwa Mahajjata 1,571 Miliyoyin Naira

  • Watanni bakwai bayan kammala aikin hajjin bara, Hukumar alhazai ta shirya mayarwa wasu mahajjata kudin da suka biya
  • Hukumar a jihar Jigawa ta ware N95m domin ba wasu mahajjata 1,571 saboda rashin cika musu wasu daga cikin hakkokinsu
  • Shugaban hukumar a Jigawa, Ahmad Labbo ya ce kowane mahajjaci daga cikinsu zai samu N61,080 na aikin hajjin 2023 da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Hukumar Alhazai a jihar Jigawa za ta mayar da makudan kudi ga mahajjata da suka gudanar da aikin hajji.

Hukumar ta dauki matakin mayarwa mahajjata 1,572 kudi har N95m kan abubuwan da ba a cika musu ka'ida ba yayin aikin hajjin 2023.

Dubban mahajjata za su samu N95m daga hukumar alhazai
Hukumar alhazai a Jigawa za ta dawowa da mahajjata 1,571 kudinsu har N95m. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Asali: Facebook

Mahajjata 1,571 za su caba a jihar Jigawa

Shugaban hukumar alhazai a jihar, Ahmad Labbo shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe dattijo mai shekaru 85 bayan karɓar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labbo ya bayyana haka a birnin Dutse inda ya ce sun dauki matakin saboda wasu hakkoki da mahajjatan ba su samu ba a hajjin shekarar 2023.

Shugaban hukumar ya ce kowane mahajjaci daga cikin 1,571 zai samu N61,080 wanda jimillar kudin ya kai N95.1m.

Yawan kudin da hukumar ta warewa mahajjata

"Yawan kuɗin da za a mayar na mahajjatan 2023 ya kai N95m ga mahajjata 1,571 a jihar Jigawa."
"Idan aka raba tsakanin mahajjata 1,571 kowane mahajjaci zai samu N61,080 kenan a jihar."

- Ahmad Labbo

Labbo ya ce jami'ansu daga ofisoshin yanki sun bukaci mahajjatan da abin ya shafa su kawo asusun bankunansu domin biyansu hakkokinsu.

Shugaban hukumar alhazai ya je Majalisar Tarayya

Kun ji cewa kwamitin majalisar wakilai ya zargi hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da tafka badakaloli iri iri a harkar gudanar da aikin hajji.

Shugaban kwamitin da aka kafa ya binciki hukumar, Sada Soli ya jefa zargin a lokacin da shugaban hukumar ya bayyana a gabansu.

Kara karanta wannan

Daga zama Minista, mai dakin Ojukwu ta dage sai Tinubu ya saki Nnamdi Kanu

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya tabbatar da zargin majalisar na cewa ana tafka badakala a hukumarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.