Bayan Shekaru 18, Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Ranar Gudanar da Ƙidaya a Najeriya
- Shugaban hukumar kidayar jama’a ta kasa, Nasir Isa Kwarra, ya bayyana cewa kidayar Najeriya za ta gudana a shekarar 2025
- Kwarra ya ce rashin kidaya tun 2006 ya haifar da matsaloli wajen raba albarkatu, samar da kiwon lafiya da kuma mace-macen mata
- Toyin Saraki, shugabar gidauniyar WFA ta jaddada bukatar haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin cimma burin shirin ICPD
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban hukumar kidayar jama’a ta kasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, ya sanar da cewa za a gudanar da kidayar jama’a a Najeriya a 2025.
Kwarra ya bayyana hakan yayin bikin cika shekara guda na taron Nairobi kan kidaya da ci gaban al’umma ICPD a Abuja ranar Alhamis.
Hukumar NPC ta shirya gudanar da kidaya
Duk da shawarar Majalisar Dinkin Duniya na cewa a gudanar da kidaya duk bayan shekaru 10, Najeriya ta yi kidayar karshe a 2006, a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabata ta dage kidayar 2023, inda ta nemi gwamnatin da ta ci zabe ta jagoranci aiwatar da aikin kidayar.
Kwarra ya jaddada cewa jinkirin gudanar da kidayar na kawo cikas musamman wajen tsara shirye-shirye da rabon albarkatu a yankunan karkara.
Abin da rashin kidaya ke jawowa Najeriya
Ya ce rashin bayanan sahihiyar kidaya na hana isar da ayyukan kiwon lafiya yadda ya kamata, wanda ke haifar da mutuwar mata masu juna biyu da kananan yara.
“Muna da niyyar inganta lafiya musamman a bangaren haihuwa, kawar da cin zarafin jinsi, da tabbatar da an ba mata da matasa damarmaki.”
- A cewar Kwarra.
Toyin Saraki, shugabar gidauniyar Wellbeing Foundation Africa, ta yi alkawarin ci gaba da yakin neman sauyi a matakin kasa da duniya, tare da cimma muradun ICPD.
"Muna jiran umarnin Tinubu" - NPC
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kidaya ta kasa (NPC), ta ce ta tanadi duk abinda ya kamata domin gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje.
Kwamishinan NPC a Adamawa, Clifford Zirra wanda ya bayyana hakan ya ce umarnin shugaba Bola Ahmed Tinubu kawai hukumar ke jira domin fara kidayar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng