Shugaba Buhari ya ware N10b domin a kidaya yawan mutanen Najeriya
- Gwamnatin Buhari ta ware kudi da nufin a fara aikin kidayar ‘Yan Najeriya
- NPC za ta soma aikin EAD domin sharar fagen gano yawan mutanen kasa
- Shugaban Hukumar NPC, Oyetunji ya ce za a soma wannan aiki kafin zabe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar wa hukumar kidaya ta kasa watau NPC, kudi domin aikin EAD a wasu bangarorin Najeriya.
The Nation ta ce Mai girma Muhammadu Buhari ya bada umarnin a warewa hukumar NPC Naira biliyan 10 domin kidaya a kananan hukumomi 546.
Ana yin wannan aiki na EAD ne domin a tsara yadda za a ji dadin kidaya mutanen da ke Najeriya.
KU KARANTA: Buhari ya yi magana game da salon nadin kujeru
Haka zalika shugaban kasar ya bada umarni a ware Naira biliyan 4.5 a kasafin kudin shekara mai zuwa domin ayi aikin kidayar mutanen da ke kasar nan.
Mukaddashin shugaban NPC na kasa, Dr. Eyitayo Oyetunji, ya shaidawa ‘yan jarida wannan lamari a safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2020.
Dazu ne a hedikwatar hukumar NPC, Dr. Eyitayo Oyetunji ya yi wa manema labarai bayanin inda aka kwana game da aikin sharar fagen kidayar da za ayi.
“Shugaban kasa ya bada umarnin a sa Naira biliyan 4.5 a cikin kasafin kudin 2021 domin kammala wannan aiki a shirin kidayar da za ayi.” Inji Oyetunji.
KU KARANTA: Mashahuran da su ka halarci daurin Auren Aliyu Atiku da Fatima Ribadu
“Babu shakka wannan gagarumar nasara ce da aka samu a gwamnatin shugaba Buhari, ta fahimci amfanin alkaluma, musamman adadin ‘yan kasa.”
Ya ce adadin yawan ‘yan Najeriya ya na da muhimmanci wajen tsare-tsare da kason arzikin kasa.
Dazu mun kawo maku karin bayanai game da abin da ya sa duka Jihohi su ka maka Shugaban kasa a kotu, su na kukan Buhari ya toye masu hakkinsu.
Wasu Lauyoyi sun bayyana makasudin da ya sa Gwamnoni su ka yi wa Buhari fito-na-fito.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng