'Da Yanzu Na Zama Dan Shaye Shaye,' Obansajo Ya Tuno Rayuwar da Ya Yi a Baya
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi kira ga matasa su guji amfani da miyagun ƙwayoyi, "domin suna lalata rayuwa"
- Obasanjo ya kuma tariyo yadda ya taba yin yunkurin fara shan taba sigari amma ta kusa bashi matsala, inda dole ya hakura da shanta
- A zantawarmu da Kwamared Zainab Dass, ta bukaci iyaye da su sanya ido kan 'ya'yansu musamman wadanda ke karatu a jami'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gargadi matasa da ɗalibai da su guji tu'ammali da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ba su da amfani ga rayuwa.
Ya yi wannan kiran ne a taron ‘Fly Above The High’ da kungiyar RAN ta shirya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Abeokuta, jihar Ogun.
Obasanjo ya magantu kan safarar kwayoyi
Obasanjo ya nuna damuwa kan yawaitar amfani da miyagun ƙwayoyi a Najeriya da Afirka ta Yamma, yana mai kiran matasa su nisanci wannan ɗabi’a, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya ce a jagorancin kwamitin yaki da shaye shaye na Afirka ta Yamma da yake yi, ya gano cewa yankin ne ya zama cibiyar tu'ammali da ƙwayoyi.
Ya bayyana cewa bincikensu ya gano miyagun ƙwayoyi daga Latin America suna zuwa Afirka ta Yamma kafin su isa Arewacin Amurka da Turai, kuma ana amfani da su a yankin.
Obasanjo ya tuno da lokacin shan tabarsa
Obasanjo ya ba da labarin yadda ya fara shan taba a ƙuruciya amma a karshe ya gamu da tari mai tsanani, wanda ya tilasta shi gujewa wannan mummunar ɗabi’ar.
"Da ace na dage da shan tabar, watakila da yanzu na zama rikakken dan shaye shaye. Da zarar shan kwaya ya bi maka jiki, to yana wahala kafin ka daina."
- A cewar Obasanjo.
A yayin da yake kira ga matasa da su nemi taimako daga masana kiwon lafiya da kuma kauracewa shan kwayoyi, ya jaddada cewa:
"Babu abin da miyagun ƙwayoyi za su yi maka face lalata rayuwarka."
Shugabar dalibai ta yi jan hankali
Zainab Mohammed Dass, tsohuwar mataimakiyar shugaban dalibai a jami'ar Abuja (UNIABUJA) ta ja hankalin dalibai, musamman na jami'a da su guji shaye shaye.
Kwamared Zainab Dass ta ce abin takaici ne yadda dalibai ke lalata rayuwarsu a lokacin da ya kamata su mayar da hankali wajen yin ilimi mai zurfi.
"Dalibai kan biyewa kawayen banza, suna shaye shaye da yawace yawace, sai an kammala zangon karatu a basu 'C/O' haka za su yi ta zama a makaranta ba tare da sun gama ba.
"Wannan matsalar maza da mata ce, kuma ya zama wajibi ga iyaye su rika sanya ido kan yaransu, wannan zai taimaka wajen rage yawan masu shaye shaye."
- A cewar Kwamared.
"Daure mashaya ba shi da amfani" - Obasanjo
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya nemi da a daina daure kananan mashayan wiwi, a cewarsa hakan na mayar da su manyan masu aikata laifuka.
Obasanjo ya ce a lokacin da aka daure dan wiwi a gidan yari, yana haduwa da mutane da dama wadanda laifinsu ya wuce nasa, wanda a karshe za su koyar da wancan dabi'unsu.
Asali: Legit.ng