Wata tsohuwa 'yar shekara 95 da ta fara shan tabar wiwi tun tana 'yar shekara 10 a duniya

Wata tsohuwa 'yar shekara 95 da ta fara shan tabar wiwi tun tana 'yar shekara 10 a duniya

- Wata tsohuwa 'yar shekara 95 ta bayyana cewa shan tabar wiwi ita ce ta jawo mata tsawon rayuwa a duniya

- Matar 'yar kasar Jamaica ta bayyana cewa tun tana 'yar shekara goma iyayenta suka koya mata shan tabar wiwin

- Ta ce kuma tana da tabbacin baza ta daina ba har sai ta bar duniyar nan

Tun bayan lokacin da ta fara shan tabar wiwi tana shekara 10, Melita Gordon ta bayyana cewa ba za ta taba daina sha ba har mutuwar ta.

A cewar matar 'yar kasar Jamaica, ta ce idan ta daina shan tabar wiwin za ta mutu ne. Wannan magana da tayi ta samu goyon bayan likitan ta wanda ya kara fayyace dangantakar matar da tabar wiwi, ya ce tabar tana daya daga cikin abubuwan da suka sa ta yi tsawon rayuwa.

Maganar da tayi ta samu goyon bayan likitan ta wanda ya kara fayyace dangantakar matar da tabar wiwi, ya ce tabar tana daya daga cikin abubuwan da suka sa ta yi tsawon rayuwa.

KU KARANTA: Hotunan Aisha Buhari da matan shugabannin kasashen Afirka a kasa mai tsarki

Melita Gordon, 'yar gidan Richard Gordon da Michelle Jones ta bayyana cewa tun bayan lokacin da iyayenta suka koya mata shan tabar wiwin har yanzu ba ta daina ba.

Duk da dai ta shafe shekaru sama da 85 tana shan tabar wiwin kullum, ba kowanne mutum ne yake murna da wannan dabi'ar tata ba, musamman 'yarta, wacce ta dauki lokaci tana rokar mahaifiyarta ta daina shan tabar wiwin.

Sai dai wasu masana sun yi na'am da bayanin Melita Gordo na cewa tabar wiwin tana daya daga cikin dalilan da yasa tayi tsawon rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel