Daure mashayan wiwi ba shi da amfani — Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bukaci a daina daure kananan mashayan wiwi, a cewarsa hakan na mayar da su manyan masu aikata laifuka.
Obasanjo ya bayyana cewa a lokacin da aka daure shi a gidan yarin Najeriya ya hadu da mutane da dama wadanda laifinsu bai wuce "kama su da kullin wiwi ba, amma aka daure su".
A cewarsa, "Idan matashi ya soma shan wiwi kuma aka kama shi aka daure a gidan kurkuku zai fito a matsayin babban mai aikata laifi. Maimakon haka, ya kamata a ba su kulawa ta musamman; a ji ta bakinsu, a rarrashe su domin su daina aikata wannan mumunan dabi’a.”
Tsohon shugaban na Najeriya na magana ne a daidai lokacin da wata kungiya mai suna The Global Commission on Drug Policy wacce fitattun shugabannin duniya ke cikinta, ta yi kira a sake yin nazari kan yadda ake magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
KU KARANTA KUMA: Rundunar Kwastam na Tin Can ta yi alfahari da kamun N287.6b da ta yi a 2017
Kungiyar, wacce ta fitar da sabon rahoto kan yadda ake tunkarar yaki da miyagun kwayoyi, ta ce tsangwamar da ake yi wa masu shaye-shayen kwayoyin tana yin kafar-ungulu a yakin da ake yi da kwayoyin.
Obasanjo ya kasance shugaban kungiyar reshen Afirka ta Yamma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng