Bankin Duniya Ya ba Najeriya Sabon Bashin N8.5bn, Masana Sun Hango Babbar Matsala
- Gwamnatin tarayya ta samu rancen $500m daga Bankin Duniya domin inganta ayyukan kamfanonin rarraba wuta (Discos)
- Kudin zai tafi wajen gyara layukan wuta, kara karfin na'urori, da siyan mitoci don inganta rarraba wutar lantarki a kasar
- Kamfanin TCN ya bayyana yadda kudaden za su taimaki kamfanonin rarraba wutar da kuma daidaituwar wutar a fadin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta samu rancen $500m daga Bankin Duniya domin karfafa kamfanonin rarraba wutar lantarki (Discos).
Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da samun kudin a ranar Alhamis, wanda aka ware domin shirin gyaran bangaren rarraba wutar lantarki (DISREP).
An samu rancen ne ta karkashin shirin bayar da mita na shugaban kasa, domin bunkasa karfin kudi da fasaha a bangaren rarraba wutar, a cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $500m
A cewar kamfanin TCN, wani bangare na kudin zai tafi ne wajen ayyukan tuntuba domin ganin an aiwatar da shirin ba tare da tangarda ba.
TCN ya sanar da cewa:
"Bankin Duniya ya amince da bayar da rancen dala miliyan 500 domin taimakawa wajen aiwatar da shirin DISREP."
Babban burin shirin DISREP shi ne inganta ayyukan kudi da fasaha na kamfanonin rarraba wutar lantarkin Najeriya.
TCN ya ce sabon bashin kudin zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen inganta ayyukan kowanne kamfani na rarraba wutar lantarkin.
Yadda sabon bashin zai taimakawa Discos
Shirin zai inganta samar da wutar lantarki, rage asara, kara adadin abokan hulda da kuma inganta hanyoyin sa-ido kan rarraba wutar.
Kudin zai kuma tafi ne kan gyaran matsakaita da kananan layukan rarraba wutar lantarki da kuma gyara manyan na'urorin rarraba wutar.
Shirin zai ba Discos damar samun sababbin hanyoyin siyan wutar lantarki daga masu samar da wuta da kuma samar da na'urori na zamani.
Haka kuma, kudin zai taimaka wajen siyan mitocin abokan hulda da na kasuwanci da kuma jigilar su zuwa rumbunan Discos domin rarrabawa.
Duba sanarwar TCN a nan kasa:
Karbo bashi: Masana sun gargadi Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa masana sun gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan ci gaba da karbo bashin da take yi, suna masu cewa hakan matsala ne ga Najeriya.
Tsohon dan majalisar wakilai, Dachung Bagos, ya bayyana damuwarsa kan karuwar bashin da Najeriya ke karbowa, yana tambayar gwamnati ta yadda za ta iya biyan bashin.
Asali: Legit.ng