'Ya Kafa Tarihi': Uba Sani Ya Bar Kujera, An Samu Sabuwar Gwamna a Jihar Kaduna

'Ya Kafa Tarihi': Uba Sani Ya Bar Kujera, An Samu Sabuwar Gwamna a Jihar Kaduna

  • An samu sabuwar gwamna a jihar Kaduna a wani bangare na ayyukan bikin ranar kananan yara ta duniya ta shekarar 2024
  • Rahotanni sun ce Gwamna Uba Sani ya bar kujerarsa, tare da dora 'yar shekara 15, Miss Hussaina Adam a kan kujerar
  • Gwamnar Kaduna ta kwana daya, Miss Hussaina ta ba yara tabbacin cewa za ta basu ingantaccen ilimi da kare hakkokinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bar kujerarsa tare da mikata ga wata yarinya 'yar shekara 15, Miss Hussaina Adam.

Miss Hussaina Adam, gwamnan Kaduna ta kwana daya, ta ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta kare hakkokin kananan yara.

Gwamnar Kaduna ta kwana 1 ta yi alkawarin kare hakkokin kananan yaran jihar
'Yar shekara 15 ta dare kujerar gwamnan jihar Kaduna, ta yiwa yara albishir. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Miss Hussaina Adam ta dare kujerar gwamnan ne a wani bangare na ayyukan bikin ranar yara ta duniya ta shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Zanga zanga : Gwamnatin Kano ta mika yara 76 ga iyayensu, an ba kowane yaro tallafin kudi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yar shekara 15 ta zama gwamnar Kaduna

Gwamna Hussaina Adam ta ba da tabbacin kare hakkin kananan yaran ne a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim a ranar Talata.

Ta yi jawabin ne yayin da yara da suka kai mata ziyarar ban girma bisa jagorancin jami’an asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).

Kwamishiniyar ayyuka da ci gaban jama’a ta jihar Kaduna, Hajia Rabi Salisu da sauran jami’an gwamnati ne suka takewa Gwamna Hussaina baya a ranar.

Gwamna Hussaina Adam ta baiwa kananan yaran tabbacin samun ingantacciyar rayuwa da samun damammaki a karkashin gwamnatinta.

Gwamnar Kaduna ta yiwa yara albishir

Gwamnan jihar Kaduna ta kwana daya, ta ce:

"Mun daura damarar kawo karshen yunwa a tsakanin yara da kuma mayar da yara zuwa makaranta. Aikinmu ne magance matsalolin da yaran Kaduna ke fuskanta.
"A karkashin wannan gwamnatin, dukkanin yaran Kaduna za su samu ingantaccen ilimi kuma za mu tabbatar kowanne yaro ya samu damar da ta dace."

Kara karanta wannan

Ma'aikata sun yi barazanar shiga yajin aiki a Arewacin Najeriya, bayanai sun fito

Gwamna Hussaina ta yi kira ga hukumomin gwamnati, kungiyoyi da masu hannu da shuni da su hada karfi da karfe domin kare hakkokin yara.

Yarinya ta hau kujerar shugabar majalisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar shekara 16 Ms Isabel Anani ta dare kan kujerar shugaban majalisar wakilai a wani yunkuri na nuna makomar 'ya'ya mata a Najeriya.

Shugaban majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya kafa tarihi ta hanyar sauka daga kujerarsa tare da dora Ms Isabel a ranar 10 ga watan Oktoba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.