'Ba Za Mu Zabi Bare ba': Yaron Tinubu Ya Fara Fuskantar Kalubale daga Matasan Legas

'Ba Za Mu Zabi Bare ba': Yaron Tinubu Ya Fara Fuskantar Kalubale daga Matasan Legas

  • Wata kungiyar matasan Legas ta bayyana cewa babu gurbi ga wadanda ba 'yan asalin jihar ba a zaben gwamna na 2027
  • Kungiyar ta bukaci Seyi Tinubu, dan shugaban kasa Bola Tinubu, da ya karkatar da burinsa na zama gwamna zuwa jihar Osun
  • Shugaban kungiyar, Abdul Kareem Whyte, ya bayyana cewa za su yi aiki don dakile takarar wadanda ba 'yan asalin Legas ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Wata kungiyar matasa 'yan asalin Legas ta shawarci Seyi, yaron Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya nemi gwamna a jihar Osun maimakon Legas.

Kungiyar ta yi alkawarin yin tsayin daka domin dakile duk wanda ba dan asalin Legas ba da ke shirin tsayawa takarar gwamna a 2027.

Kungiyar matasan Legas sun caccaki dan Shugaba Bola Tinubu kan shirin tsayawa takarar gwamna
Kungiya ta bukaci Seyi Bola Tinubu da ya nemi takara a Osun amma ba jihar Legas ba. Hoto: @STinubu
Asali: Twitter

Kungiya ta fara adawa da Seyi Tinubu

Kara karanta wannan

An samu rabuwar kai a APC kan zargin sakataren gwamnatin Tinubu da ƙabilanci

Shugaban kungiyar, Abdul Kareem Whyte, ya bayyana wannan matsayar ne ranar Alhamis, 21 ga Nuwamba, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayar kungiyar ta biyo bayan goyon bayan da wata kungiyar shugabannin matasan Najeriya(CONYL) ta ba Seyi Tinubu na tsayawa takarar gwamna a 2027.

Abdul Kareem Whyte ya ce babu gurbi ga wadanda ba 'yan asalin Legas ba a zaben gwamna na 2027 domin za su kare 'yancin asalin jihar.

'Ka nemi takara a Osun' - Whyte ga Seyi

Jaridar Vanguard ta rahoto Whyte na ikirarin cewa tun daga 1999, mutum daya ne kacal daga cikin 'yan asalin Legas da ya taba mulkar jihar.

Ya ce akwai gurbin gwamna da Seyi zai iya nema a jihar Osun, inda zai yi amfani da 'yancinsa ba tare da wata matsala ba.

A cewarsa, idan mutanen Owerri, Imo, suna sha’awar amfana da kwarewar Seyi Tinubu, za su iya tura shi ya gaji Gwamna Hope Uzodinma.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samo mafita kan yaki da ta'addanci a Afrika

Ana so dan Tinubu ya nemi gwamna

Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar shugabannin matasan Najeriya (CONYL) ta ce Seyi, dan Shugaba Bola Tinubu ne wanda take so ya zama gwamnan Legas.

Kungiyoyin matasan da suka fito daga shiyyoyi shida na kasar nan sun bayyana cewa akwai bukatar Seyi Tinubu ya nemi kujerar da babansa ya hau a kakar zabe ta 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.