Gwamnan APC Ya Kafa Tarihi, Ya Gabatar da Kasafin Naira Tiriliyan 3 ga Majalisa

Gwamnan APC Ya Kafa Tarihi, Ya Gabatar da Kasafin Naira Tiriliyan 3 ga Majalisa

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya gabatar da kasafin 2025 ga majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis
  • Rahoto ya nuna cewa Gwamna Sanwo-Olu ya gabatar da Naira tiriliyan 3 a matsayin kasafin kudin domin dorewar ayyuka
  • Kasafin kudin zai maida hankali kan ilimi, kiwon lafiya, tsaro, kiyaye muhalli da samar da ababen more rayuwa a jihar Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gabatar da Naira tiriliyan 3.005 ga majalisar dokoki ta jihar a matsayin kasafin kudin jihar na 2025.

Kasafin kudin, wanda aka sanya wa suna "Kasafi mai dorewa," ya mayar da hankali kan manyan ayyukan ci gaba don bunkasa tattalin arzikin jihar.

Gwamnan jihar Legas ya yi magana yayin da ya gabatar da kasafin 2025
Gwamnan Legas, Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin 2025 ga majalisar dokokin jihar. Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Mai tallafawa Gwamna Sanwo-Olu ta fuskar kafofin watsa labarai na zamani, Jubril A. Gawat ya sanar da hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince Bola Tinubu ya karɓo bashin Naira tiriliyan 1.77

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kasafta kasafin Legas na 2025

Cikakken bayani game da kasafin kudin ya nuna cewa an ware Naira tiriliyan 1.7 domin manyan ayyuka, inda aka fi maida hankali kan gine-gine.

A bangaren ayyukan yau da kullum kuwa, gwamnan ya ware Naira tiriliyan 1.2 na kasafin domin kula da kudaden gudanarwar gwamnati.

Gwamna Sanwo-Olu ya jaddada muhimmancin aiwatar gine ginen ababen more rayuwa, tare da samar da kasafin da za a amfana da shi na dogon lokaci.

Gwamna ya yiwa al'ummar Legas albishir

Ya tabbatar wa al’ummar Legas cewa kasafin kudin zai maida hankali kan bangarori masu muhimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya, tsaro, da kiyaye muhalli.

The Nation ta ruwaito gwamnan na cewa kasafin kudin yana nuna jajircewar jihar wajen bin tsarin kula da kudi da magance manyan matsalolin ci gaba.

Kasafin kudin yanzu yana jiran tantancewa da amincewa daga majalisar dokoki ta jihar Legas.

Kara karanta wannan

'Kisan mutane 17': Gwamna a Arewa ya hana Fulani daukar fansa bayan harin Lakurawa

Gwamna Inuwa ya gabatar da kasafin 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar da kasafin kudin 2025 gaban majalisar dokokin jihar.

Gwamna Muhammadu Inuwa ya gabatar da Naira biliyan 320.11 a matsayin kasafin kudin jihar inda ya mayar da hankali kan gine-ginen ababen more rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.