An gano muhimmin abu guda da Legas ta fi ragowar biranen duniya da shi

An gano muhimmin abu guda da Legas ta fi ragowar biranen duniya da shi

Wani sakamakon bincike na musamman a kan tattalin arziki da ake fitar wa kowacce shekara ya bayyana cewar akwai saukin rayuwa a birnin Legas na Najeriya fiye da ragowar manyan birane da ke duniya.

Faris, babban birnin kasa Faransa, ya samu cigaba a fannin tsadar rayuwa bayan ya matsa daga mataki na biyu a bara zuwa mataki na daya a bana.

Ana gudanar da irin wannan bincike duk shekara domin taimakon ma su tafiye-tafiye, musamman irin na kasuwanci, domin sanin irin shirin da za su yi yayin da za su ziyarci wani babban birni a duniya.

Masu binciken na auna tsadar rayuwa ne ta hanyar kwatanta farashin kayayyakin masarufi da more rayuwa da farashin su a manyan biranen nahiyar Turai.

Birnin Caracas na kasar Venuzuela da Damascus a kasar Syria, sun fi kowanne birni da ke duniya arahar rayuwa. Sai dai an alakanta arahar rayuwa wa wadannan birane da yanayin yaki da su ke ciki.

An gano muhimmin abu guda da Legas ta fi ragowar biranen duniya da shi
Legas
Asali: Getty Images

Birnin Legas da ke Najeria na mataki na shida a jerin biranen duniya da rayuwa ke da matukar sauki.

Kayan masarufi irin su biredi, barasa, da abinci na da matukar araha a Legas idan aka kwatanta da wasu manyan biranen duniya irin su Singapore, Paris, Honkong da sauran su.

DUBA WANNAN: Abin da likitoci su ka fada bayan ‘yar Najeriya ta haifi ‘ya’ya 6 a asibitin Amurka

Biranen duniya 10 da ke da tsadar rayuwa su ne; Singapore (Singapore), Paris (Faransa), Hong Kong (China), Zurich (Switzerland), Geneva (Switzerland), Osaka (Japan), Seoul (Koriya ta Kudu), Copenhagen (Denmark), New York (Amurka), Tel Aviv (Isra'ila), da Los Angeles (Amurka).

Biranen duniya 10 da rayuwa ta fi sauki su ne;

1. Caracas a kasar Venezuela

2. Damascus a kasar Syria

3. Tashkent a kasar Uzbekistan

4. Almaty a kasar Kazakhstan

5. Bangalore kasar India

6. Karachi a kasar Pakistan

6. Legas a Najeriya

7. Buenos Aires a kasar Argentina

7. Chennai kasar India

8. New Delhi ta kasar India

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel