Kasafin kudi: Sanwo Olu ya sa hannu, Gwamnatin Legas za ta kashe N1.163tr

Kasafin kudi: Sanwo Olu ya sa hannu, Gwamnatin Legas za ta kashe N1.163tr

- Gwamnatin Legas ta sa hannu a kan kasafin kudin shekara mai zuwa

- Jihar Legas za ta batar da Naira Tiriliyan 1.163 a shekarar nan ta 2021

- Wannan kudi ya zarce abin da rabin jihohin Arewa za su batar a bana

A ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020, mai girma gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sa hannu a kan kundin kasafin kudin shekarar 2021.

Jaridar Vanguard ta rahoto Babajide Sanwo-Olu ya rattaba hannu a kasafin kudin N1.163 da ake sa ran gwamnatin Legas za ta kashe a shekarar bana.

An ware 40% na wannan kasafin kudi ta yadda za a kashe biliyan N460 wajen biyan albashi da alawus da sauran abubuwan batarwan yau da gobe.

Gwamnatin Legas za ta kuma batar da Naira biliyan 702.9 wajen yin ayyukan more rayuwa a 2021.

KU KARANTA: Za a shigar da kasafin 2021 ya zama doka a Najeriya

A duk jihohi babu wani gwamna da ya yi kasafin kudin da ya kama kafar na Legas, abin da jihar za ta kashe ya nunka na jihohi da-dama a dunkule.

Kamar yadda mu ka fahimta, kasafin kudin jihar Legas ya fi karfin abin da rabin jihohin Arewa za su kashe a wannan shekara ta 2021 da aka shiga jiya.

Sai an hada kasafin jihohin Nasarawa, Benuwai, Kogi, Gombe, Yobe, Kebbi, Zamfara, Jigawa da Adamawa, sannan za a samu abin da Legas za ta kashe.

Abin da wadannan jihohi tara da aka ambata su ka yi kasafi a bana shi ne N115bn, N10bn, N134bn, N116bn, N140bn, N107bn, N141bn, N145bn, da N156bn.

KU KARANTA: Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin jihar Kano na shekarar 2021

Kasafin kudi: Sanwo Olu ya sa hannu, Gwamnatin Legas za ta kashe N1.163tr
Gwamna Jide Sanwo Olu Hoto: Twitter/Jidesanwoolu
Asali: Twitter

Jimillar wannan kudi da wadannan jihohin Arewa za su batar a wannan shekara shi ne N1.184tr.

A gefe guda kuma, manyan gwamonin Arewa; Nasir El-Rufai da Aminu Bello Masari sun yi kasafin Naira biliyan 236 da Naira biliyan 280 a shekarar nan.

Kwanaki kun ji cewa jihohin Kwara, Jigawa da Bauchi su na sa ran kashe N493.48b a 2021.

Alkaluma sun nuna a cikin jerin jihohin da suka fi dogara da kasafin FAAC da gwamnatin tarayya ta ke rabawa duk wata, akwai jihohin yankin Arewa bakwai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng