'Tabarbarewar Dangantaka': Masana Sun Hango Illar Rashin Nada Jakadun Najeriya
- Har yanzu Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai naɗa sababbin jakadu ba tun bayan dawo da tsofaffin gida a watan Satumbar 2023
- Masana diflomasiyya sun nuna damuwa kan rashin nada jakadun, wanda ke rage tasirin Najeriya wajen hulɗa da kasashen waje
- Minista Yusuf Tuggar ya ce jinkirin ya samo asali ne daga matsalar kuɗi, amma gwamnati tana aiki domin magance matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shekara guda da wata ɗaya kenan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo da jakadun Najeriya gida, kuma har yanzu bai naɗa sababbi ba.
Tun bayan dawo da su ranar 2 ga Satumba, 2023, ofisoshin jakadancin Najeriya 109 a kasashen waje sun kasance babu cikakken wakilci na jakadanci.
An hango illar jinkirin nada jakadu
Masana harkokin diflomasiyya da tsofaffin jakadu sun ce rashin jakadu na rage tasirin dangantakar Najeriya da sauran kasashe, a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bayyana cewa masu kula da ofisoshin yanzu ba su da matsayin da ya dace don ganawa da ministocin harkokin waje na kasashen da suke ciki.
A matsayinsu na daraktoci a ma’aikatar gwamnati, suna fuskantar iyakoki wajen gudanar da ayyukan da ke buƙatar amfani da ikon jakadu.
Masana sun caccaki rashin nada jakadu
Jakada Suleiman Dahiru ya caccaki jinkirin, yana mai cewa ya kamata a nada sababbin jakadu kafin a kira tsofaffin gida.
Ya yi gargadin cewa jinkirin zai iya hana a nada wasu jami’an diflomasiyya da suka cancanta saboda shekarunsu ya kusa kai na ritaya.
Wani tsohon jakada ya ce wasu ƙasashe na iya ƙin hulɗa da ƙananan jami’ai, abin da zai ƙara tsananta dangantakar Najeriya da su.
Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama na ƙasa da ƙasa, amma ana buƙatar jakadu domin tabbatar da cewa Najeriya ta ci moriyarsu.
Abin da ya jawo jinkirin nadin jakadu
Tun da fari, mun ruwaito cewa ma’aikatar harkokin waje ta ce rashin kuɗi da tsauraran tantancewa ne ke jawo jinkiri wajen naɗin jakadu a yanzu haka.
Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar ya tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa, duk da ƙalubalen, gwamnati na aiki kan matsalar kuma za ta warware ta nan gaba.
Asali: Legit.ng