Alakar Diflomasiyya: Gwamnatin kasar Iran za ta kafa Jami’o’i a Najeriya

Alakar Diflomasiyya: Gwamnatin kasar Iran za ta kafa Jami’o’i a Najeriya

Kasar Iran ta bayyana ma Najeriya cewa a shirya take ta kafa jami’o’I a Najeriya don bukatar daliban Najeriya dake ficewa kasashen waje don neman ingantaccen ilimi, inji rahoton Daily Trust.

Jakadan kasar Iran a Najeriya, Mosteza Rahimi Zarchi ya bayyana cewa idan har kasashen biyu suka amince da kulla yajejeniyar, hakan zai samar da rassan jami’o’in kasar Iran a Najeriya.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya amince da naɗin sabon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jakadan ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 39 da juyin juya halin da aka yi a kasar, wanda ya samar da kafa gwamnatin shi’a, inda ya kara da cewa jami’o’I a kasar Iran na da matukar inganci, sa’annan kudadensu basu da wani tsauri.

“Muna fata zamu fadada dangatakar dake tsakanin Najeriya da Iran zuwa ga cigaban kimiyya da fasaha da kuma bangaren ilimi, hakan zai samar da isassun makarantu don amfanin daliban Najeriya dake neman karatun digiri da digirgir.” Inji shi

Bugu da kari, Zarchi yace kasar Iran na da bukatar ganin ta fadada alakarta da Najeriya zuwa bangaren iskar mai da gas, gine gine da samar da gidajen zama, sa’annan ya tabbatar da saura kiris wadannan yajejeniya su kai ga gaci.

Daga karshe Jakadan yace kasar Iran ta samu gagaruman cigaba a bangaren siyasa, tsaro, tattalin arziki, ilimi da kuma harkar magani, a shekaru 39 da suka gabata, kumaya bada tabbacin zasu cigaba da kokari wajen magance matsalar tsatstsauran ra’ayi a fadin duniya gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng